Yanda ‘Yan Sanda Suka Ci Zarafin Wani Direban Tasi
Wani direban tasi ya bayyana cutarwar da ‘yan sanda suka yi masa har yayi watanni 7 a gidan gyaran hali.
A cewarsa, sun shiga motarsa, suka ki biyansa kudin mota, daga ya bukaci hakkinsa sai suka kulla masa tuggu da makirci.
‘Yan sandan sun hadashi da wasu masu fasa bututun man fetur, inda kotu ta yanke musu hukunci tare.
Wani direban tasi a jihar Ogun, Mayowa Ayodele, ya bayyana yadda ‘yan sanda suka adana shi a gidan gyaran hali na tsawon watanni 7, saboda ya bukaci su biya shi kudin mota.
Ayodele, ya bayyana yadda ya fuskanci cin zarafi da cutarwar a hannun ‘yan sanda a Abeokuta, ranar Laraba.
Read Also:
A cewarsa, ‘yan sanda 4 suka yi shatar motarsa a ranar 7 ga watan Maris, 2018, amma suka ki biyanshi, Premium Times ta wallafa.
Bayan ya bukaci su biya shi hakkinsa suka kulla masa sharrin da yayi sanadiyyar daure shi a gidan gyaran hali.
A cewarsa, cikin ‘yan sanda da suka cutar da shi sun hada da Buhari Yusuf, Ehimere Anthony da wasu 2 da ba zai iya tuna sunayensu ba.
Kamar yadda yayi bayani, “Na dauke su tun daga Mowe zuwa Magboro, na kuma mayar da su Shagamu.
Bayan na ajiye su, sai na bukaci su biyani hakkina, N4500, amma suka ki. “Suka ce ai gwamnati suke yi wa aiki. Bayan na matsa, sai suka ce wa shugabansu ya daure ni, na fasa bututun man fetur.”
Kamar yadda Ayodele yace, an kulleshi a Motor Traffic Division da ke Shagamu.
Sai da yayi kwana 16 kafin a kai shi babbar kotu da ke Oke Mosan da ke Abeokuta inda aka yanke masa hukuncin fasa bututun man fetur.