Akwai ‘Yan Siyasa da ke Aiki Tukuru Wajen Ganin Sun Bata Sunan Yusuf Bichi – DSS
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce akwai ‘yan siyasan da ke aiki tukuru wajen ganin sun bata sunan hukumar.
DSS ta ce, musamman shugabanta, ana ta kokarin ganin an shafa masa bakin fenti kan aikin da ya yake yi.
Ana cece-kuce a Najeriya game da yadda hukumar DSS ke shirin kame wasu ‘yan siyasa da abokansu a kasar.
Najeriya – Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayyana cewa, akwai wani shiri da wasu gurbatattutun ‘yan siyasa ke yi na ganin sun bata sunan babban daraktanta, Yusuf Bichi da wasu manyan jami’anta, TheCable ta ruwaito.
Wannan na fitowa ne a cikin wata sanarwa da kakakin DSS, Peter Afunanya ya fitar, inda yace wasu ‘yan siyasa a ciki da wajen gwamnati na kokarin kawo cikas ga aikin hukumar na tsayawa tsayin daka ga dakile barna.
Afunanya ya kuma ce ‘yan siyasan Najeriya na amfani da kungiyoyin farar hula da kungiyoyi masu zaman kansu wajen bata sunan Bichi ba gaira ba dalili.
Hukumar ta DSS ta ce ya kamata ‘yan kasa su guji duk wani batu da ke ake yi na ganin an shafa bakin fenti ga manyan jami’anta, musamman daraktan.
Kafafen yada labarai na bata sunan Bichi, inji hukumar DSS
Read Also:
Hakazalika, sanarwar ta zargi wasu gidajen jaridu da kafafen yada labarai da kirkirar rubuce-rubuce da ke bata sunan Bichi da ahalinsa a kwanakin nan.
Saboda haka, hukumar tace tana zuba ido, kuma za ta dauki matakin da ya dace a lokacin da ya dace kan masu yada bayanan karya game da hukumar, kuma ta ce babu abin da zai hana aiwatar da ayyukanta.
Wani bangaren sanarwar ya ce:
“Hukumar DSS, don haka na fatan sanar da jama’a da su kaucewa wadannan batutuwa kuma su yi watsi da duk wani bakin fenti da ake son shafawa katarin DG.”
Hakazalika, Afunanya ya ce, hukumar za ta ci gaba da tunkarar duk wata barazana ta tsaron kasa tare da aiki tukuru wajen tabbatar da an yi zabe cikin lumana.
Yadda batutuwa suka taso game da DG na DSS
A baya kadan, kungiyoyin farar hula a Najeriya sun tada magana cewa, hukumar ta DSS na kokarin tarfa gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele bisa zargin ta’addanci, The Guardian ta ruwaito.
Baya ga haka, kungiyar kiristoci ta CAN ta ce akwai hannun ‘yan siyasa wajen kitsa kwamushe gwamnan babban bankin na CBN.
Ana ta yada cewa, batun kama gwamnan n CBN na da alaka da siyasa tun bayan da bankin ya ba da umarnin sauya fasalin kudi tare da sanya sabbin ka’idojoji ga kashe yawon kudi a kasar.
Hakazalika, an yi ta cece-kuce game da yadda ake zargin matar shugaban na DSS ta umartar cin zarafin dan takarar gwamnan NNPP a jihar Kano.