Premier: Man United za ta Karbi Bakuncin Man City

 

A ranar Asabar ne Manchester United za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan da ake hasashen zai yi zafi wanda kuma za a kalla a ko’ina a faɗin duniya.

United ta yi nasara a wasanni takwas a jere kuma za ta iya kai wa ga mafi dadewa a gasar tun bayan da Alex Ferguson ya yi ritaya a matsayin koci a 2013.

City da ke mataki na biyu da maki hudu a saman United ta sha kashi a hannun Southampton a gasar cin kofin Carabao a ranar Laraba.

Kocin City Pep Guardiola ya ce a yanzu Man United na cikin ganiyarta wanda hakan a bayyane yake.

United na dab da ɗaukar aron ɗan wasan Burnley Wout Weghorst amma ba zai iya buga wasa ba saboda yana buƙatar a yi masa rijista da misalin karfe 12:00 a ranar Juma’a.

Sai dai da wuya Anthony Martial ya buga wasan saboda raunin da ya ji a kafarsa, don haka Marcus Rashford, wanda ya ci kwallaye bakwai a wasanni shida da suka wuce, zai iya buga a matsayin ɗan wasan gaba.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here