NNPC Tana Tafka Asara Wajen Sayar da Mai Saboda Umarnin Gwamnatin Tarayya Kan Batun Tallafi – Timipre Sylva

 

 

Karamin Ministan Fetur a Najeriya ya ce NNPC tana tafka asara wajen sayar da mai saboda umarnin gwamnatin Tarayya kan batun tallafi.

Timipre Sylva ya shaida hakan ne adaidai lokacin da dillalan man fetur ke cewa suna fuskantar karanci mai lamarin da ka iya sake ta’azzara wahalar man har zuwa watan Yuni, saboda shirin gwamnati na janye tallafi baki ɗaya a wannan watan.

Jaridar PUNCH ta rawaito ministan na waɗannan maganganu ne a Abuja lokacin bayyana abubuwan da suka aiwatar tsakanin 2015 zuwa 2023 karkashin mulkin Muhammadu Buhari.

A makon da ya gabata, Ministar kuɗi da tsare-tsare, Zainab Ahmed ta ce gwamnati ta ware naira tiriliyan 3.6 na tallafi fetur zuwa Yunin 2023.

Sai dai PUNCH ta rawaito Sylva a lokacin zantawa da ‘yan jarida a Abuja, na cewa tallafin babban nauyi ne, sai dai kuma wajibi ne ga NNPC da aka daurawa alhakin tafiyar da harkokin fetur a kasar ta ci gaba da daukar asara.

Gwamnatin Najeriya a ranar Litinin ta bayyana cewa ta zuba hanayen jari a matatun mai hudu da ke shirin soma ayyukansu a sassa daban-daban a faɗin Kasar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here