‘Yan Takarar Shugaban Kasa na 2023 Sun sa Hannu Kan Zaman Lafiya

 

‘Yan takarar shugaba kasa a zaben 2023 na Najeriya sun sa hannu kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a birnin Abuja.

An ga fuskokin ‘yan takara kamar na jam’iyyar Labour, Peter Obi da mataimakin dan takarar jam’iyyar APC Kashim Shettima da Atiku Abubakar, dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya.

Karin ‘yan takarar sun hadar da na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso da Hamza Al-Mustafa na jam’iyyar AA, akwai Omoyele Sowore na jam’iyyar AAC.

Kwamitin tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaben Najeriya karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) ne ya shirya wannan taro don sa hannu a kan yarjejeniyar

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here