Ina da Yara Uku a Jami’o’in Gwamnatin – Chris Ngige
Chris Ngige, ministan kwadago da ayyuka, ya ce yana da yara 3 a jami’o’in gwamnati.
Ministan ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a kan yajin aikin ASUU.
Ya ce ASUU bata isa tace bai damu ba, don ya tsaya tsayin-daka a kan lamarin.
Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, yace yana da yara 3 a jami’o’in gwamnati da ke kasarnan, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Ministan ya fadi hakan a wata tattaunawa da Arise TV suka yi dashi a kan yajin aikin malaman jami’a, wanda ya dakatar da karatun yara da dama.
Read Also:
Ngige ya ce yana daya daga cikin iyayen daliban jami’o’in gwamnatin Najeriya, yana zargin ‘yan kungiyar ASUU da tura yaransu jami’o’in kudi.
A cewarsa, “Ina da yara 3 a makarantun gwamnati.
A makarantun gwamnati suke; ba jami’o’i masu zaman kansu ba.
Ba kamar ‘yan kungiyar ASUU ba duk sun tura yaransu jami’o’in kudi, ni kuwa ina da 3 anan.
Don haka ina da ruwa da tsaki a makarantun gwamnati.
“Don haka idan ASUU ta ce ‘yan siyasa basu damu da lamarin ba saboda sun tura yaransu kasashen waje, Chris Ngige ya damu, saboda yaransa suna karatu a nan kasar, duk da 2 daga cikinsu suna da shaidar zama Amurka amma na zabi su zauna nan tare da ni.
“Don haka, ASUU ba su isa su zargeni da rashin kishin kasa ba.
Ina yin iyakar kokarin ganin na taimaki jami’o’in kasar nan.”