Yadda Wasu Matasa Sukai wa Wani Barawo

Wasu matasa da suka kama barawo sun taimake shi da abin sha mai zaki domin kawai ya samu karfi su kara jibarsa.

Matasan sun kama matashin dumu-dumu da laifn sata a Takoradi da ke kasar Ghana.

Bayan barawon ya fita daga hayyacinsa saboda duka, matasan da ke dukansa sun bashi lemo don ya farfado su sake yi masa rubdugu a karo na biyu.

Rahotanni sun nuna yadda wasu matasan ƙasar Ghana suka taimaki wani mutum ta hanyar dawo masa da kuzarinsa saboda su jibge shi a karo na biyu bisa zarginsa da aikata halin ɓera.

Acewar rahotanni, wasu matasa a Takorodi ta kasar Ghana sun bawa wani ɓarawo abin sha mai ƙara ƙarfi da kuzari, bayan ya galabaita, kawai don ya dawo hayyacinsa su ƙara dukansa a karo na biyu.

Wani ganau ba jiyau ba wanda ya watsa labarin, ya ce an kama ɓarawon dumu dumu da laifin sata.

Maimakon miƙa shi ga hukuma ko rundunar ƴansanda, sai matasan unguwar suka ɗauki doka a hannunsu, suka yi masa dukan kawo wuƙa.

Bayan sun fahimci ya galabaita kuma dukan ya daina shiga jikinsa, sai sukayi sauri suka bashi abin sha mai ƙara kuzari da ƙarfi na “Rush” don ya dawo hayyacinsa su ɗora daga inda suka tsaya.

Wannan ganau shine ya yaɗa hoton lokacin da matasan suka zagaye ɓarawon yana tsaka da shan lamurjen ƙarin kuzarin.

Anyi rubutu a jikin hoton kamar haka”Barka da zuwa Takoradi, kasar Ghana, gurin da aka zane wani ɓarawo, sannan mu ka bashi abin sha mai sinadarin ƙarin kuzari na Caffeine saboda kawai mu ƙara jibgarsa.Wannan shine irin karamcinmu.Babu inda ya kai Taadi”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here