Yaran Asari Dokubo Sun Dira Harabar Kotun Zaɓen Shugaban ƙasa a Abuja
Yaran Asari Dokubo, tsohon shugaban tsagerun Neja Delta sun dira harabar kotun zaɓen shugaban ƙasa a Abuja.
Matasan ɗauke da alluna sun je kotun ne domin nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
A yau ne dai kotun zaɓen za ta yanke hukuncinta kan ƙararrakin da Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar na ƙalubalantar nasarar Tinubu.
FCT, Abuja – Tsohon shugaban tsagerun yankin Neja Delta, Asari Dokubo, ya tattaro matasa ɗauke da alluna a safiyar ranar Laraba sun dira harabar kotun ɗaukaka ƙara, rahoton PMnews ya tabbatar.
Read Also:
Matasan dai sun dira harabar kotun ne domin nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a yayin da ƴan Najeriya ke jiran hukuncin da kotun za ta yanke a shari’ar zaɓen shugaban ƙasa na ranar, 25 ga watan Fabrairun 2023.
Menene abin da matasan suka je yi a kotun
Matasan dai suna sanye ne da baƙaƙen kaya da jajaye waɗanda aka sanya sunan Asari Dokubo a jiki.
Matasan suna ɗauke da alluna yayin da su ke rera waƙoƙi da yin raye-raye.
Saƙonnin da ke jikin allunan na cewa:
“Ƴan Neja Delta na goyon bayan nasarar da ƴan Najeriya sama da miliyan 200 suka ba Shugaba Tinubu.”
“Shugaba Tinubu yana son Neja Delta’ da mun gode Tinubu bisa dawo da ma’aikatar Neja Delta”.