Aikin Hajji Zai Kara Tsada – Hukumar Kula da Alhazai ta kasa

 

Hukumar kula da Alhazai a kasar nan ta tabbatar da za a karin kudi sosai wajen zuwa aikin hajji.

Shugaban NAHCON ya ce tsarin da CBN ta kawo na daidaita kudin kasar waje ne sanadin tsadar.

Zikrullah Hassan ya bukaci hukumomin da ke jihohi su fara karbar N4.5m a kan kowace kujera.

Abuja – Hukumar da ke kula da Alhazai a Najeriya (NAHCON) ta fara shirye-shiryen yanke kudin da za a biya domin sauke farali a hajji mai zuwa.

A rahoton da Daily Trust ta fitar a safiyar Laraba, an ji hukumar NAHCON ta yi umarni ga hukumomin jin dadin Alhazai a jihohi su karbi N4.5m.

Shugaban NAHCON na kasa, Zikrullah Hassan ya bayyana cewa farashin aikin hajji zai karu saosai a sakamakon daidaita kudin waje da aka yi.

Hajjin bana: NAHCON ta yi zama da shugabannin jihohi

Malam Zikrullah Hassan ya shaida haka ne bayan ya zanta da shugabanni da sakarorin hukumomin jin dadin Alhazai na duk jihohi a Abuja.

Ganin Dalar Amurka ta tashi zuwa akalla N750 a bankin CBN, hukumar tarayyar ta ce ba ta da tabbaci kan kudin da za ta karba hannun maniyyata.

Za a fara karbar Naira miliyan 4.5 daga hannun mutane amma Hassan ya ce farashin zai iya canzawa idan Dala ta tashi ko ta karye a kasuwar canji.

Hajji zai tashi daga N2.9m zuwa N5m Legit.ng Hausa ta na da labari a shekarar da ta gabata da aka saida Dala a N450, maniyyata sun fara biyan N2m, daga baya su ka cika kusan N1m.

Muddin aka fara biyan fiye da N4m domin kama kujeru, da alama a karshe alhazai su kashe sama da N5m, sai dai idan Naira ce ta farfado a kasuwa.

Jawabin shugaban Hukumar NAHCON Dole in fada maku kudin hajjin shekarar nan zai yi tsada.

Wannan abu ne da dole mu shirya masa, tun daga yau.

Ba ina cewa za mu iya sanin farashin tun daga yau ba, amma wajibi ne mu san da cewa hajjin zai yi tsada sosai.

Dalili kuwa shi ne an wuce zamanin rangwamen kudin kasar waje. Yanzu da mu ke magana, $1 ta na a N740 ne.

Saboda haka idan aka yi lissafi da Dalar zuwa aikin hajji a bara, za ku iya tunanin miliyan nawa za a kara a kujera.

– Zikrullah Hassan

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com