A Shirye Nake na bi Duk Abinda Gwamnati ta Zaɓa Tsakanin Zaman Lafiya da Yaƙi – Bello Turji

 

Sanannen ɗan bindigan nan, Bello Turji, ya nuna damuwarsa bisa harin da jirgin sojoji ya kai gidansa a Zamfara.

Turji yace harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutanensa da dama duk da ya tuba ya rungumi zaman lafiya tsawon watanni.

Ɗan bindigan ya yi gargaɗin cewa a shirye yake ya bi duk abinda gwamnati ta zaɓa tsakanin zaman lafiya da yaƙi.

Zamfara – Ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Bello Turji, yace cin amana ne harin da Sojojin Najeriya suka kai sansaninsa a jihar Zamfara.

Jaridar The Cable ta ruwaito yadda wani luguden wutan rundunar sojin saman Najeriya ya yi sanadin kashe gomman yan ta’adda a mafakar Turji.

Bayanai sun nuna cewa ‘yan fashin dajin sun halarci wurin ɗaura aure tare da Bello Turji lokacin da jirgin NAF ya yi ruwan bama-bamai a wani yankin ƙaramar hukumar Shinkafi.

Sai dai an ce Turji ya tsallake rijiya da baya. A wani faifan Audio da jaridar PRNigeria ta samu, ƙasurgumin ɗan bindigan ya nuna ɓacin ransa kan harin jirgin duk da ya amince ya watsar da ayyukan ta’addanci.

“Bamu kai hari ba an samu zaman lafiya tsawon watanni biyar amma yanzu da Sojoji suka farmaki gidanmu, muna jin an ci amanar mu musamman ganin yadda muka rasa mutane a harin Jirgin yaƙi.”

“Watanni 5 da suka shude bamu kai hari ko kashe mutun ɗaya ba a yankin Shinkafi. Sakamakon haka Noma da sauran harkokin kasuwanci sun fara farfaɗo wa ba tare da fargaba ba.”

“Na ji kunya da aka ambaci sunana bayan wasu ‘yan fashin daji da ‘yan ta’adda sun kai hari. Bayan gidana da aka tasa aiki, mafi yawan gidajen mutanen da ba ruwansu a Jejin harin jirgin ya taɓa su.”

– Bello Turji, a faifan maganar da ya fito.

A shirye muke mu rungumi zaman lafiya – Turji Ɗan bindigan ya ƙara da cewa a shirye yake ya rungumi zaman lafiya mai ɗore wa matukar gwamnati ba so take ya sake ɗaukar makami ba.

“Zaman lafiya ya zarce darajar komai kuma a shirye nake na rungumi zaman lafiya matuƙar ba gwamnati na kokarin tunzura ni na koma fagen yaƙi ba.

A shirya nake a zauna lafiya ko a yi yaƙi.” “Duk abinda gwamnati ta zaɓa a shirye muke mu ba su ninkinasa, zaman lafiya ko yaƙi.”

Bello Turji ya tuɓa – Sanata Nasiha Wannan cigaban ya faru ne ƙasa da wata ɗaya, bayan Sanata Hassan Nasiha, mataimakin gwamnan Zamfara yace Turji ya karɓi shirin zaman lafiya da gwamnati ta zo da shi.

Nasiha yace ƙasurgumin ɗan bindigan ya daina kai wa al’umma hari, ya koma kan ‘yan ta’addan da suka ƙi amince wa su tubarwa Allah.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here