Mambobin PDP da SDP a Jihar Oyo Sun Sauya Sheka Zuwa APC

 

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi babban kamu a jihar Oyo gabannin babban zaben 2023.

Mambobin manyan jam’iyyun adawa ta PDP da SDP da dama sun sauya sheka zuwa jam’iyyar mai mulki a kasar.

Sun sha alwashin yin aiki domin ganin dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar, Sanata Teslim Folarin ya lashe zabe.

Oyo – Wasu mambobin jam’iyyar siyasa a jihar Oyo sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabannin babban zaben 2023.

Masu sauya shekar sun samu tarba a ranar Asabar yayin wani taron jam’iyyar da ya gudana a makarantar sakandare na Elekuro, Ogbere a yankin Ona-Ara da ke jihar.

Wadanda suka jagoranci taron na maraba da zuwa sune, Sanata Teslim Folarin, dan takarar gwamna na APC a jihar da Dr Yunus Akintunde, dan takarar sanata mai wakiltan Oyo ta tsakiya, PM News ta rahoto.

A madadin Folarin, shugaban hukumar caca ta kasa, Alhaji Fatai Ibikunle, ya yiwa masu sauya shekar maraba da zuwa APC.

Ibikunle ya basu tabbacin samun adalci da daidaito a sabuwar jam’iyyarsu, yana mai alkawarin cewa za su amfana daga kowace dama game da jin dadin ‘ya’yan jam’iyya ba tare da wariya ba.

Ya ce:

“Ina maku maraba da zuwa jam’iyyarmu, APC, a matsayin sabbin mambobi kuma ina bakun taccin samun dukkanin yancin da sauran mambobinsu zasu samu.

“Za mu tabbatar da ganin cewa kun amfana daga kowace irin dama game da jin dadin ‘ya’yan jam’iyya ba tare da son kai ba.”

Ya bukaci sabbin mambobin da su tattaro jama’a don nasarar yan takaran APC a zaben 2023, rahoton Vanguard.

Mogaji Akinjide, wanda ya jagorancin masu sauya sheka daga PDP, ya ce sun ji dadin kwarya-kwaryar da Folarin ya shirya masu.

Yayinda Elder A Kalejaye, wanda ya jagoranci masu sauya sheka daga SDP, ya ce kokarin Folarin da zamowarsa dan takarar gwamna na APC ne yasa suka sauya sheka.

A cewarsa, nasarar APC a zaben 2023 zai amfani karamar hukumar Ona-Ara dama jihar baki daya. Folarin ya jinjinawa masu sauya shekar, yana mai cewa sun yanke hukunci mai kyau ta hanyar dawowa APC.

A halin yanzu, ya yi alkawarin tafiya tare da masu sauya shekar a dukkan harkokin jam’iyyar da kuma tabbatar da ganin cewa sun amfana daga damammakin.

Dan takarar gwamnan ya bukace su da su tafi ungunninsu mabanbanta zannan su dunga halartan tarukan jam’iyyar akai-akai don samun karin bayani game da jam’iyyar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here