ENDSARS: Yadda Rikicin Zanga-Zangar ya Shafi ‘Yan Arewa a Kudancin Najeriya
Wasu da ake zargin masu zanga-zanga ne sun kashe mutum biyu tare da ƙona dukiyoyi a birnin Aba na Jihar Abia a jiya Laraba.
Lamarin ya faru ne yayin da mutanen ɗauke da adduna da katakwaye suka far ma wata kasuwar kayan gwari, wadda akasari Hausawa ne.
Read Also:
BBC ta tuntuɓi Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Abia, SP Geoffery Ogbonna, sai dai ya ce lokacin da aka kira shi lokacin barcinsa ne.
Gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a biranen Aba da Umuhia, sai dai matakin bai sanyaya gwiwar masu zanga-zangar ba.
Alhaji Haladu Imam mai albasa na daga cikin shugabannin ‘yan arewa mazauna Aba kuma ya shaiada wa BBC cewa an far musu ne da misalin ƙarfe 4:30 na rana.
“Mun ji ƙarar harbin bindigogi kuma sojojin da ke wurin gaba ɗaya sun gudu,” in ji shi. “Sun ƙona ƙanana da manyan motoci kusan 30.”
A birnin Fatakwal ma an samu irin wannan hare-hare duk da dokar hana fita. Wani mazaunin yankin ya ce masu zanga-zangar na ƙone duk kayayyakin da suka tarar na Hausawa.