Zuwa Ga Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf…

Ya mai girma Gwamna muna masu neman taimakon ka a matsayinmu na talakawanka a wannan gari na jahar Kano mai tarin albarka. Wannan taimako ne wanda ‘yan jahar Kano da Nigeria baki daya za su yi maraba da shi. Domin kuwa Al’umma na cike da ‘kishiruwar bukatar tabbatuwa da ‘karuwar wadanda za su kula da lafiyarsu.

Mai Girma Gwamna, akwai ‘danka kuma wanda gwamnatin jahar Kano ta taimakawa lokacin da yana karatun Likitanci tun lokacin jagora “Dr Rabi’u Musa Kwankwaso”. Wanann bawan Allah yanzu haka yana fama da lalurar “ciyon hanta”. Kuma cutar taci ta cinye takai ma’kura zuwa matakin karshe. Wannan Likita mai suna Dr Ibrahim Tijjani yana cikin wani hali wanda yake bu’katuwa izuwa dashen hanta. Innalillahi!

Mai Girma Gwamna, wanann matashin likitan yana daya daga cikin likitoci masu hazaka, jajircewa, da dagewa wajan yin aikinsu yanda ya kamata. Mai girma Gwamna muna ganin barin rayuwar irin wadannan matasa ta salwanta hakika abune da Al’umma za su yi hasara matuka da gaske.

Mai Girma Gwamna wasu daga cikin manyan likitoci a jahar Kano sunyi magana da wani asibiti a ‘kasar indiya, inda wannan gagarumin aikin dashen kodar zai gudana. Wanda aka tabbatar da cewa ana bukatar Naira Miliyan Ashirin Da Biyar(N25,000,000.00). Yanzu haka Mai Girma Gwamna ‘yan uwa da abokan arziki tare da Al’ummar Nigeria na ta ‘ko’korin bada gudunmawarsu wajan ceto rayuwar wannan matashi. Amma dan Allah Mai Girma Gwamna muna bu’katar gudunmawar Gwamnati domin gaskiya wannan abune da yake bu’katar kulawa ta musamman.

Duba da yadda a kwanannan Mai Girma Gwamna ka nuna damuwar ka da halin da daliban jahar Kano suka shiga a jami’ar Bayero, hakika abun a yabane hakan. Muna ro’kon Allah ya sa shima wannan matashin Likita zai rabauta da wannan tagomashi na kabakin Alkhairi, ameeen.

Mai Girma Gwamna tuni takarda ta musamman mai ‘dauke da ‘kunshin bayanai akan komai dangane da rashin lafiyar Dr Ibrahim Tijjani ta iso cikin gidan Gwamnati. Amma muna fatan Mai Girma Gwamna ya samu wannan sako. Allah ya ‘karawa Mai Girma Gwamna lafiya da jagoranchi, ameeeeen.

Bissalam!

Dr. Khalid Sunusi Kani
Likita Kuma Mai Wayar Da Al’umma Kan Harkar Lafiya.
[email protected]

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com