Kasar Saudiyya ta Fitar da Adadin Mutanen da Zasuyi Aikin Hajji a 2021

 

Saudiyya ta bayyana cewa mutum 60,000 kacal ta amince du gudanar da aikin hajjin bana a faɗin duniya.

Ƙasar tace 15,000 daga ciki zasu fito ne daga ƙasar Saudiyya, yayin da 45,000 daga sauran ƙasashen duniya.

Saudiyya ta dakatar da gudanar da aikin hajji a bara sabida ɓarkewar cutar COVID19 a duniya Ƙasar saudiyya ta bayyana adadin mahajjatan da zasu samu damar yin aikin hajji a wannan shekarar ta 1442 byan hijira, wacce tazo dai-dai da 2021.

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da hukumar hajji ta ƙasa ta futar a shafiɓta na dandalin sada zumunta facebook ‘National Hajj Commission Of Nigeria.’

Saudiyya tace adadin mutane 60,000 ne zasu samu izinin gudanar da aikin hajji a faɗin duniya baki ɗaya

Daga cikin wannan adadin, 15,000 zasu fito ne daga cikin ƙasar ta Saudi Arabia yayin da ragowar 45,000 za’a rarrabawa ƙasashen duniya.

Hakanan hukumomin ƙasar sun fitar da dokoki dake ƙunshe da dukkan bayanan yadda aikin hajjin zai gudana. Idan baku manta ba Saudiyya ta dakatar da gudanar da aikin hajji ne sabida guje wa yaɗuwar cutar COVID19.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here