Adadin Mutanen da Suka Rasa Muhallinsu a Duniya – MDD
A karon farko, hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce adadin mutanen da rikici da tashin hankali da take hakkinsu da kaucewa gurfana gaban shari’a ya tilastawa barin gidajensu a fadin duniya sun tasamma miliyan 100.
Read Also:
Kasashen da ke sahun gaba kan wannna matsalar a nahiyar Afirka sun hada da Habasha da Burkina Faso da Najeriya da kuma jamhuriyar Dimukradiyyar Congo, kamar yadda rahoton ya bayyana a ranar Talata.
Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan ayyukan kare walwalar ‘yan gudun hijira, ya ce an samu kididdigar ne ta hanyar amfani da adadin wadanda suka bukaci ba su mafaka a wasu kasashe da suka kusan miliyan 50.