Wata Kasar Afirka Ta Kasa Biyan ƙasashen duniya Bashin su

 

Zambiya na fuskantar barazanar gaza biyan basussukan da ƙasashen waje ke bin ta bayan da ta kasa biyan fiye da dala miliyan 40 a watan da ya gabata.

A ranar Juma’a ne wa’adin da aka ƙara mata na biyan bashin ya zo ƙarshe, wanda hakan zai sa ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta gaza yin hakan tun ɓarkewar annobar cutar korona.

Dama Zambiya na fama da nauyin bashin da ƙasashen waje ke bin ta na dala biliyan 12.

Amma annobar cutar korona ta ta’azzara matsalar kuɗin da dama ƙasar ke fuskanta.

Annobar ta ƙara sanya nauyi mai wahala kan tsarin kiwon lafiyar ƙasar da fannin tattalin arzikin da ke halin taɓarɓarewa, kuma gwamnatin ta ce hakan ne ya jawo matsalolin da ƙasar ke ciki.

Amma masu suka sun zargi Shugaba Edgar Lungu da rashin iya kula da tattalin arziki sannan akwai damuwa kan yadda cin hanci yake ƙaruwa a shekarun baya-bayan nan.

Zambiya ta roƙi a ɗaga mata ƙafa wajen biyan kuɗin ruwan da ke kan bashin har sai watan Afrilun baɗi, amma masu bin ta bashin sun ƙi yarda.

Bashin ya haɗa da kusan dala biliyan uku na takardun lamuni da aka ba ta a Turai.

‘Almubazzaranci’

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa China da wasu kamfanonin Chinar sun ranta wa ƙasar kuɗi dala biliyan uku.

Bankin Raya Ƙasashe Na China ya yarda ya ɗaga ƙafa tsawon wata shida don biyan kuɗin, amma wasu masu bin bashin a wajen China sun yi ƙorafin cewa ba a fayyace ainihin dokoki da tsarin bashin Chinar ba.

A cewar wani ƙwararre kan siyasar Afirka a Jami’ar Landan Stephen Chan, a shekara biyar ɗin da suka gabata Zambiya ta yi ta almubazzaranci ta wajen tara wa kanta ɗumbin bashi.”

Ya shaida wa shirin BBC na Newsday cewa idan har babu wani shiri na biyan bashi, ba lallai a sake ɗaga musu ƙafa ba.

Ministan Kuɗi na Zambia Bwalya Ng’andu ya shaida wa Reuters a farkon makon nan cewa ƙasar na yin ”bakin ƙoƙarinta” wajen guje wa rashin cika alƙawari.

‘Buƙatun da ba su dace ba’

Sarah-Jayne Clifton, darakta a wata cibiyar da ke nema wa ƙasashe matalauta sauƙin bashi da ke Birtaniya, Jubilee Debt Campaign, ta ce masu bayar da bashin sun bai wa Zambiya ne da kuɗin ruwa mai yawa sanin cewa bashin zai zamo gagarumi.

“A yanzu barazanar kuwa ta zo, dole masu takardun lamunin su amince da rage darajar takardun” kamar yadda ta shaida wa reuters a makon nan.

“Rashin dacewa ne ga masu takardun lamunin su nemi a biya su kafatanin kuɗaɗen sannan su samu gagarumar riba kan bashin Zambiyan a yayin da ƙasar ke fama da annobar Covid-19, wata mummunar annoba da ta ragargaza tattalin arziki da jawo talauci,” a cewarta.

Amma masu takardun lamuni zuwa yanzu dai ba su bayyana goyon baya kan lattin biyan bashin ba.

Masu riƙe da takardun lamunin sun bayyana cewa ƙasar ba ta yi hoɓɓasar tattauna wa da Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF ba.

Ba Zambiya ce kaɗai ƙasar Afirka da ke fama da ƙaruwar basussukan ƙasashen waje ba, kuma sauran gwamnatoci za su sa ido sosai kan yadda masu karɓa da bayar da bashin za su wanye kan lamari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here