Somaliya: Ƙungiyar Al-Shabab ‘ta fi Gwamnatin ƙasarta Samun Kuɗin
Ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya ta al-Shabab a Somaliya na amfani da barazana da zin zarafi don samun kuɗaɗen shiga masu yawa fiye da hukumomin ƙasar, a cewar rahoto.
Masu tayar da ƙayar bayan su kan karɓi a ƙalla dala miliyan 15 duk wata, kuma fiye da rabin kuɗin suna fitowa ne daga babban birnin ƙasar Mogadishu, a cewar Cibiyar Hiraal.
Wasu ƴan kasuwar na biyan haraji ga masu tayar da ƙayar bayan da kuma gwamnatin ƙasar.
Al-Shabab ta daɗe tana yaƙi da gwamnatin ƙasar fiye da shekara 10.
Ƙungiyar na iko da mafi yawan yankin kudanci da tsakiyar Somaliya amma ta samu damar faɗaɗa ikonta zuwa yankunan da gwamnati ke iko da su a Mogadishu.
Rahoton ya bayyana yadda ƙungiyar ke tatsar kuɗaɗe daga mutanen karkara a matsayin ”zalinci.”
“Tsoro da barazanar da ake yi wa rayuwarsu su ne kawai dalilan da ke sa mutane suna bai wa al-Shabab kuɗaɗen haraji,” in ji rahoton.
A cewar Cibiyar Hiraal, ba kamar gwamnatin Somaliya ba, ita ƙungiyar al-Shabab ”tana samun rarar kuɗaɗe sosai” don yawan kuɗaɗen da take samu a shekara na ƙaruwa, a yayin da kuɗaɗen da take kashe wa kan ayyukanta bai ƙaru ba.
Dukkan manyan kamfanoni a Somaliya suna bai wa masu ikirarin jihadin kuɗaɗe, a matsayin haraji duk wata ko kuma zakkar da ta hau kansu ta shekara-shekara na kashi 2.5 cikin 100 na ribar da suke samu duk shekara, a cewar rahoton, wanda an haɗa shi ne ta hanyar yin hira da mayaƙan al-Shabab ɗin, da ƴan kasuwa a Smolaiya da jami’an gwamnati da sauran su.
Ƴan kasuwa da ke yankunan da ke ƙarƙashin ikon gwamnati – suna ƙorafin cewa suna biyan gwamnati da ƴan ta’addan haraji.
Waɗannan sun haɗa da waɗanda ke zama a Villa Somaliya da ke kusa da birnin Mogadishu, inda fadar gwamnati take, da kuma waɗanda suke biranen Bossasso da Jowhar, da ma na Kismayo da Baidoa, waɗanda dukkansu a hukumance ba sa ƙarƙashin ikon ƙungiyar.
Tashar jiragen ruwan da ke Mogadishu ita ce babbar hanyar samun kuɗaɗen shiga ta gwamnatin Somaliya. Sannan kuma ƙungiyar tana karɓar haraji kan kayayyakin da ake shiga ƙasar da su a jiragen ruwan dakon kaya daga jami’an tashar.
Cibiyar Hiraal ta ce ma’aikatan gwamnati suna bai wa al-Shabab wani kaso daga cikin albashinsu, da fatan cewa ƙungiyar za ta bar su su sakata su wala, ganin cewa suna daga cikin waɗanda suke kai wa hari.
Ma’aikatan jihohi da sauran mutanen da ke aiki a yankunan da ke ƙarƙashin ikon gwamnati su ma sun bayyana yadda mayaƙan ke tuntuɓar su ta waya don karɓar kuɗi.
Kwamandan rundunar soja na biyan al-Shabab
A yankunan da al-Shabab ke iko da su, masu karɓar haraji na ƙungiyar kan je wajen ƴan kasuwa kai tsaye su ce musu su biya haraji.
Read Also:
Wani kwamanda a rundunar sojan Somaliya ya bayyana yadda yake “aika kuɗi ga al-habab duk da yana yaki da kungiyar”.
Sojan ya ya bayyana yadda wani mutum da yake yi masa ginin gida ya bar aikin ya kuma tafi, bayan kwamandan ya ki biyan kuɗi ga ƴan ƙungiyar.
Wata mota da dake sufurin kayan gine-ginen ita ma an dakatar da ita daga zuwa wajen saboda an ce ita ma ta biya kuɗi.
“Daga ƙarshe an tilasta min ko dai in dakatar da aikin ginin ko kuma in biya al-Shabab,” a cewar kwamandan.
“Abin takaici, daga ƙarshe na biya su $3,600 sannan aka kammala aikin gidan nawa,” kamar yadda yace.
Rahoton ya ce masu da’awar jihadin suna sa ido sosai a bangaren gine-gine da ke bunkasa kamara yadda suke yi kan shigar kaya kasar.
Wani dillalin gidaje a gabar ruwan birnin Kismayo dake kudanci ya bayyana yadda ƴan ta’adda ke kiran abokan harkarsa, “suna bayar da bayanai kan harkokin kudi da suka yi sannan su umarce su su biya su wasu kudi ba tare da neman ragi ba – sannan su kuma su biya kudin kamar yadda ƴan al-shabab suka nema.”
Al-shabab wacce ta mayar da kanta wata ƙaramar gwamnati ita ce ka kaɗai ke karɓar haraji a yankunan karkara. Tana ɗaura haraji kan dabbibi da hatsi har ma kan amfani da albarkatun ruwa.
Ƙungiyar ta ƴan tawaye ta bayyana yadda a ɓangaren da take, manoman da suka biya kudin noman rani ne kawai za su iya amfani da kogi da kuma hanyoyin ruwa a gonakinsu.
“Wani manomi ya yi korafin cewa an tilasta masa biyan ‘harajin aiki’ ga motar sa ta noma har ma lokacin da ba a aiki da ita saboda talalce.”
‘Biyan kudi dole ne’
Mafi yawan ƴan kasuwa da ma’aikatan gwamnati da sauransu da suke biyan al-Shabab sun shaida wa masu binciken Hiraal cewa suna biyan kudin ne saboda tsaro.
“Biyan haraji ga al-Shabab ba ganin dama ba ne.”
Waɗanda suka ki biya ana kashe su, ko a tilasta musu rufe wuraren kasuwancinsu ko kuma su bar ƙasar.
Wasu na jin cewa ya kamata su biya kuɗin ga al-Shabab saboda ƙungiyar na saka musu. Ba kamar gwamnati ba, al-Shabab na samar musu da tsaro.
“Biyan haraji a wuraren binciken abubuwan hawa na al-Shabab na tabbatar da wuce wa salin-alin a duka fadin yankin da al-Shabab ke iko da su, da ma wuraren da ke karkashin gwamnati inda ƴan ƙungiyar ke aiki.”
Rahoton ya bayyana yadda masu da’awar jihadin suke warware rikice-rikice tsakanin ƴan kasuwa kuma suke iyakance wasu kayan da ake fitar da su kamar lemon tsami.
Hiraal ya ce hanya ɗaya da za a hana ƴan ta’addar samun kuɗaɗe ta wannan hanya ita ce ta hanyar inganta yanayin tsaro, ta yadda ƴan kasuwa da sauran mutane za su yi harkokinsu ba tare da katsalandan daga al-Shabab.
Ganin cewa ƙungiyar ta jima da kafuwa fiye da shekara 10 sannan ta ci gaba da kai hare-hare a wuraren da gwamnati ke iko da su, da alama ƙungiyar za ta ci gaba da samun kaɗaɗe, nan da wasu shekaru masu zuwa.