Amurka da Sauran Kasashe na Siyasantar da Batun Samar da Agaji a Afghanistan – Amir Khan Muttaqi
Ministan harkokin waje na Afghanistan wanda kungiyar Taliban ta nada, Amir Khan Muttaqi, ya yi kira ga Amurka da sauran kasashe da su daina mayar da batun samar da agaji ya koma na siyasa.
Ya ce Amurka babar kasa ce, kuma ya dace ta zama mai tausayawa.
Read Also:
A wani jawabi da ya gabatar a talabijin, ministan ya gode wa kasashen duniya da su ka yi alkawarin tara fiye da dala biliyan guda domin tallafa wa kasarsa.
Mista Mottaqi ya kuma ce sabuwar gwamnatin Afghanistan za ta yi duka mai yiwuwa domin taimaka wa ‘yan kasar da ke cikin mawuyacin hali ba tare da nuna bambanci ba.
A halin da ake ciki an kiyasta cewa akwai kimanin ‘yan Afghanistan miliyan uku da rabi da aka raba da muhallansu a cikin kasar.