Jawabin Ministar Kudi Kan Batun Aron Kudaden ‘Yan Najeriya da ya Dade a Bankuna
Gwamnatin tarayya za ta kara tura bukatan wasu sabbin kudade cikin kasafin kudin 2021.
Ana bukatan hakan ne domin sayawa yan Najeriya rigakafin cutar Korona.
Za’a samo wadannan kudade na ta hanyar rantan kudaden yan Najeriya dake ajiye a bankuna.
Masu kudaden dake ajiye a banki kuma suka dade basu waiwaya ba su kwantar da hankulan saboda gwamnatin tarayya ta ce zasu iya cire kudadensu duk lokacin da suke bukata.
Ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna, ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyi lokacin taron tattauna abubuwan da kasafin kudin 2021 ta kunsa jiya, Vanguard ta ruwaito.
Read Also:
“Za mu yi amfani da kudade da hannun jarin da ba’a waiwaya ba cikin wani asusu na musamman. Duk lokacin da banki ta tabbatar da mutum shine ainihin mai kusi, gwamnati za ta bashi,” ministar ta bayyana.
Mun kawo muku cewa duk da rashin amincewar masu hannun jari, gwamnatin tarayya na shirin aron kudaden yan Najeriyan da ke asusun da aka dade ba’a waiwayesu ba, da kuma kudaden masu hannun jarin da aka dade ba’a bibiya ba.
Gwamnatin zata samu daman yin hakan ne bisa dokar kudin 2020 da shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu. Karkashin sashe na 12 na dokar, an bayyana cewa za’a iya aron kudaden masu hannun jarin da ajiyan na mutanen wanda suka kai shekaru 6 ba’a waiwaya ba.
Gwamnati tace duk kudaden da ba’a bibiya ba za’a aika su wani asusun lamuni na musamman mai suna ‘Unclaimed Funds Trust Fund’.