A kalla manyan Lauyoyi 43 ne suka sha alwashin taimakawa mawallafin jaridar Daily Nigerian Malam Jaafar Jaafar da kuma Ita Daily Nigerian akan karat da Ganduje yakai su yana neman biliyan uku kan zargin bata masa suna.

Babban lauyan Daily Nigerian Muhammad DanAzumi ne ya bayyana haka ya manema labarai yayin da ake shirin fara shariah a ranar Alhamis a Babbar kotun jihar Kano.

Sai dai kuma lauyan da yake kare Gwamna Ganduje a wannan Shariah ya roki kotu da ta dage Zaman kotun zuwa wani lokaci na gaba domin bashi damar gabatar da wasu muhimmanci bayanai.

Sai dai Lauyan dake kare Jaafar Jaafar da jaridar Daily Nigerian yayi farat inda ya kalubalanci rokon lauyan Ganduje inda suka yi doguwar kuma zazzafar muhawara a tsakanin su har sai da alkali ya tsawatar musu.

 

The post Badakalar Ganduje: Lauyoyi 43 sun sha alwashin taimakawa Daily Nigerian akan Ganduje appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here