Majalisar Wakilai za ta Binciki Musabbabin Hauhawar Kayan Abinci a Najeriya
Majalisar wakilai a Najeriya ta ce za ta binciki musabbabin hauhawar kayan abinci a kasar.
Read Also:
Honorabul Adekunle Isiaka daga jahar Ogun ne ya gabatar da bukatar a gaban majalisar a zamanta na yau Laraba, inda ya ce “mafi yawan yan Najeriya ta kai ga ba sa iya sayen abincin da za su ci a rana, lura da cewa farashin kayan abincin da na gas ya ninka daga bara zuwa bana.”
A kan haka ya bukaci Shugaban majalisar Femi Gbajabiamila da ya kafa kwamitin da zai binciko inda matsalar take kafin tafi karfin magancewa.
Kayan abinci sun yi tashin gwauron zabi musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda aka rufe kasuwannin mako-mako saboda shawo kan matsalar tsaro.
Kazalika gas din dafa abinci ya ninka daga kasa da naira 4,000 zuwa naira 7,000 a tukunya mai nauyin kilo 12.