Ta’aziyyar Ahmed Joda: Shugaba Buhari ya Dira Jahar Adamawa

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Yola, jahar Adamawa a ranar Juma’a, 20 ga Agusta, domin gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Ahmed Joda.

Buhari ya dira ne misalin karfe 10 na safe tare da tawagarsa.

Hadimin Buhari na gidajen rediyo da talabijin, Buhari Sallau, ya bayyana haka.

Dirarsa ke da wuya, Buhari ya garzaya fadar Lamidon Adamawa.

Rasuwar Alhaji Ahmad Joda

Tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Najeriya lokacin mulkin Soja kuma mutum na farko da Buhari ya ba mukami bayan nasara a 2015 , Alhaji Ahmed Joda, ya mutu.

Ya rasu ne ranar Juma’a, 13 ga Agusta a Yola, babbar birnin jahar Adamawa. Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

Alhaji Ahmed Joda ya cika ne yana mai shekaru 91 a duniya.

Joda ya yi karatunsa a Najeriya da kuma Birtaniya inda ya halarci Kwalejin Pitmans da ke birnin London daga 1954 zuwa 1956.

Ya rike kujeran sakataren din-din-din lokacin gwamnatin mulkin soja ta Janar Yakubu Gowon (Mai murabus).

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here