Shugaba Buhari ya Mayar da Martani Kan Kisan Mutane a Goronyo Dake Jahar Sokoto

 

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, karshen ‘yan bindiga ya zo, kuma za a ragargaje su nan kusa.

Ya bayyana haka ne yayin da ya yi Allah wadai da harin ‘yan bindiga a wani yankin jahar Sokoto.

Ya kuma bayyana cewa, sojoji na sake shirin don ci gaba da ganowa da kuma hallaka ‘yan bindigan.

Abuja – Daily Trust ta rawaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan bindiga cewa su kasance a shirye don murkushe su ya zo kusa.

Shugaban ya yi wannan gargadin ne a ranar Litinin 18 ga watan Oktoba yayin da yake mayar da martani kan kisan sama da mutane 30 a Goronyo, Jahar Sakkwato ranar Lahadi

Buhari, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, ya ce kwanakin ‘yan bindiga a kirge suke saboda karfin da sojojin Najeriya ke samu ta hanyar samun kayan aiki da sauran bukatu.

Ya yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya:

“Kada su yanke kauna saboda wannan gwamnatin ta himmatu fiye da kowane lokaci wajen kare ‘yan Najeriya daga kungiyoyin masu aikata kisan gilla wadanda ba sa girmama kimar rayuwar dan adam.”

Shugaban ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda harin Goronyo ya rutsa da su sannan ya yi kira ga mutane da su ci gaba da hakuri yayin da sojoji ke nemo yadda za su kai wa wadannan ‘yan bindiga hari.

Ya ce:

“Lokacin halakar ku yana tafe saboda ba za ku sake samun wurin buya ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here