EndSars: Wanan Irin Mataki Shugaba Buhari ya Dauka Don kawo ƙarshen zanga-zangar?

Tun bayan da zanga-zangar kawo ƙarshen rundunar ƴan sanda ta Sars ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a Najeriya, wasu ƴan ƙasar ke ta nuna fargaba kan abin da ka je ya zo.

Wasu da dama na ganin lokaci ya yi da ya kamata Shugaba Buhari ya dauki mataki kan lamarin, duk da cewa a makon farko na zanga-zangar shugaban ya yi magana tare da ɗaukar matakin rusa rundunar ta Sars, wadda ita ce buƙatar masu zanga-zangar.

Sai dai bayan rushe rundunar gwamnati ta kafa sabuwa mai suna SWAT don maye gurbinta, hakan ya sa masu zanga-zangar ci gaba da kira a rushe ta ita ma, sai dai har yanzu Shugaba Buhari bai ƙara cewa uffan ba.

A biranen Legas da Abuja inda zanga-zangar ke ci gaba da bazuwa, lamarin da ke saka mazauna biranen cikin tasku na takurawa zirga-zirga da walwalarsu, inda a ranar Litinin da yamma zanga-zangar ta rikiɗe zuwa rikici a wasu unguwannin.

To shin ya kamata shugaban ƙasar ya sake yin wani abu ne bayan wanda ya yi? Me ya kamata ya yi a wannan gaɓar?

Waɗannan su ne tambayoyin da muka mika wa masu sharhi kan al’amuran yau da kullum da kuma masu bin mu a shafukan sada zumunta, ga kuma abin da suke ganin ya kamata shugaban ya yi
Kabiru Sufi, mai sharhi ne kan al’amuran siyasa sannan malami ne a kwalejin share fagen shiga jami’a da ke Kano, wanda ya shaida wa BBC cewa bai kamata gwamnati ta yi gaggawar kafa sabuwar rundunar SWAT ba.

Kabiru Sufi, mai sharhi ne kan al’amuran siyasa sannan malami ne a kwalejin share fagen shiga jami’a da ke Kano, wanda ya shaida wa BBC cewa bai kamata gwamnati ta yi gaggawar kafa sabuwar rundunar SWAT ba.

Ga abubuwan da yake ganin sun kamata gwamnatin Shugaba Buharin ta yi:

Kamata ya yi gwamnati ta dauki mataki na wucin gadi kamar kafa kwamiti na manyan mutane masana da masu shari’a kan kawo sauye-sauye a harkar ƴan sanda
Tun da masu zanga-zangar na ƙara bijiro da buƙatu, gwamnati tana da zaɓi kan matakan da ya kamata ta ɗauka kamar haka
Shugaban kasa na iya fitowa ya zauna da masu zanga-zangar kuma ya gabatar da sabbin sauye-sauye kamar yadda ya yi alƙawari, kamar alƙawarin tabbatar da sauyi ga aikin ƴan sanda
Shugaban na iya fitowa ya yi jawabi mai ƙarfi wanda zai nuna gwamnati ta damu kuma za ta
maganin matsalolin tare da sanar da sabbin matakai – wannan zai iya sa abubuwa su lafa
Gwamnati na iya daukar matakai na dakile zanga-zangar ganin yadda ta fara rikiɗewa daga ta lumana a wasu wuraren
Gwamnati na iya ɗaukar mataki na lamuna ba tare da wani abu ya biyo baya wanda zai saɓawa abin da dimokradiyya ta yarda da shi ba.
Shi kuma Dr Abubakar Kari masanin siyasa kuma mai sharhi a Najeriya, sannan malami a Jami’ar Abuja cewa ya yi:

Ya kamata gawamnati ma ta fahimci buƙatun masu zanga-zangar domin yanzu manufar zanga-zangar ta sauya daga Endsars ta koma kamar ta siyasa
Gwamnati na iya abu uku – cika alƙawarin da gwamnati ta yi na ɗaukar matakai game da ƴan sanda. Idan har za a aiwatar da su za a samu ci gaba ya kamata a ce an aiwatar da su – ya kamata gwamnati ta kyautata aikinsu da kuma tabbatar da suna daraja mutane
Gwamnati dole ta ɗauki matakai wajen tabbatar da zanga-zangar ba ta zama tashin hankali ba – domin kullum rikiɗewa take tana tayar da hankalin mutane
Shugaban kasa na iya fitowa ya yi jawabi don sanyaya ran mutane da hankalinsu, duk da cewa dai ya yi taƙaitacce a makon da ya gabata.
Sai dai a ganin Dr Kari, su ma masu zanga-zangar akwai matsalolin da ya kamata su magance daga ɓangarensu.

”Matsalar har yanzu masu zanga-zangar ba su da shugabanni- wanda wannan ya kawo ruɗani saboda ba su da manufa ko alƙibla.

”An biya buƙatunsu na rusa rundunar tare da kafa wata – ya kamata su yi wa gwamnati uzuri su ba da lokaci kan matakan da gwamnati ta ce za ta ɗauka.

”Yanzu kullum manufar zanga-zangar canzawa take. Zanga-zangar a wasu wuraren ta koma ta tashin hankali, an ƙona ofishin ƴan sanda da ɓalle gidajen yari da kuma kai wa gwamnati hari,” in ji Dr Kari.

A shafin Facebook na BBC Hausa Ahmad Abubakar ya wallafa cewa: ”Shugaba Buhari ya sauke dukkan shugabannin tsaro ya sa sababbi. Ya yi wa ƴan sanda garambawul. Ya sa ASUU su koma makaranta ta hanyar biyansu abun da suke nema.

”Ya canza salon mulkinsa ta hanyar yin adalci ga kowa ba tare da ƙabilanci ko aƙida ko ɓangaranci ba. Ya rage albashin ƴan majalisu da ministoci baki daya. Ina ga waɗannan su ne maƙasudin wannan fitina. Allah Ya kawo mana karshenta.”

Jabir Nuhu Liman ya ce: ”Ya zauna da shugabanni masu zanga-zangar, ya saurari buƙatunsu, sai a yi compromise (wato gwamnati ta yi hakuri ta biya musu wani sashin abun da suke so, abin da ya saɓawa hankali kuma su haƙura). Kafin ƴan Arewa su fara tasu zanga-zangar da gaske su ma.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here