Bola Tinubu: Mahimman Abubuwa 10 da Babban ɗan Siyasar ya ce Game da Zanga-Zangar EndSARS

Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce zanga-zangar kyamar rundunar SARS ta sa gwamnati za ta yi gyara ga tsarin ƴan sanda a ƙasar.

A wata sanarwa, Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zangar su dakatar da zanga-zangar bayan tilasta rusa rundunar SARS da kuma gabatar da buƙatunsu, waɗanda ya ce gwamnati na nazari a kai.

Zanga-zangar da ake kira EndSARS ta ci gaba da bazuwa a sassan Najeriya, inda yanzu ta shiga mako na uku.

Abubuwa 10 da Tinubu ya faɗa game da zanga-zangar sun haɗa da:

1. A kwanaki goma sha biyu da suka gabata, kasarmu ta fuskanci zanga-zangar matasa daga birane da dama, waɗanda suka nuna rashin jin daɗinsu kan take haƙƙin ɗan Adam da suka hada da azabtarwa, kwace, muzgunawa da tsoratarwa har ma da kisa da jami’an rundunar yaki da fashi da makami ta SARS suka aikata.

2. Buƙatun neman sake fasalin aikin ƴan sanda da matasa masu zanga-zangar ke yi yana cikin burin ƴan Najeriya da ke cikin taken ƙasa.

3. Irin wannan hukunci da rashin bin doka ba su dace da tsarin mulkin dimokuradiyya ba.

4. Rashin hukunta SARS ya kasance ƙalubalen da matasa suka yi fafutika da ƙwarin guiwa kuma suka yi nasara wanda ya haifar da tunanin sake fasalin tsarin ‘yan sanda a kasar.

5. Dole ne masu zanga-zangar su amince cewa matakin da gwamnatin Shugaba Buhari ta ɗauka ya cancanci yabo, ba wai kawai rusa SARS ba har da yarda da bukatu biyar da suka haifar da zanga-zangar. Wannan abin yaba wa ne ga sauraren ƙorafin matasan.

6. Duk da yake a baya gwamnati ba ta aiwatar da sauye-sauyen da ta yi alkawari ba, amma yadda wannan gwamnatin ta yi hanzarin sauraren buƙatun masu zanga-zangar a wannan karon yana nuna cewa akwai kyakkyawan sauyi daga gare ta da kuma wani sabon yanayi na gaggawa.

7. Dole ne a bai wa gwamnati dama don ta aiwatar da sauye-sauyen da masu zanga-zangar suka nema. Tabbas ba za a iya aiwatar da su ba nan take.

8. Masu zanga-zangar sun samu nasarori masu yawa cikin kankanen lokaci. Amma kuma ya kamata su yi hankali kada su ɓata rawarsu da tsalle musamman yadda wasu zauna-gari-banza da ƴan daba ke neman kwace zanga-zangar don tayar da hankali da cin zarafin mutane.

9. Dole ne sai masu zanga-zangar sun yi hankali kada su samar da wani yanayi na tarwatsa tsarin dimokuradiyya da ya ba su dama da ‘yancin yin zanga-zanga.

10. Ina kira ga shugabannin addini da su yi kira ga mabiyansu su janye zanga-zangar a yanzu a samu zaman lafiya.

Tinubu ya yi waɗannan kalaman ne bayan shafe kusan mako biyu ana zanga-zangar neman gwamnatinsu ta APC ta gaggauta kawo sauyi a tsarin aikin ɗan sanda.

Wasu na ganin yana cikin waɗanda ya kamata su fito su yayyafa wa zanga-zangar ruwa tun kaddamar da ita amma sai yanzu. Ko da yake a baya ya fito ya yi bayani game da zanga-zangar.

Kalaman tsohon gwamnan na Legas Bola Tinubu na zuwa ne bayan zargin da wasu ke yi cewa yana cikin waɗanda suke ɗaukar nauyin masu zangar ta adawa da rundunar SARS domin kawo ruɗani a gwamnatin Buhari, zargin da jagoran na APC ya musanta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here