Corona ta Kashe Jagoran Makamin Nukiliyar Pakistan, Abdul Qadeer Khan
Masanin wanda ake kira ‘jagoran makamin nukiliyar Pakistan’ ya rasu ne yana da shekara 85 a duniya bayan ya kamu da corona.
Ƴan ƙasar Pakistan suna kallon Abdul Qadeer Khan a matsayin wani gwarzon kasarsu saboda sanya Pakistan zama ƙasar musulmi ta farko da ta mallaki nukiliya a 1998.
Shugaban Pakistan Imran Khan, ya ce ya samar da tsaro ga barazanar makwabciyar ƙasar mai makamin nukiliya, Indiya.
Sai dai ya sha suka kan yadda ya kwarmata sirrin makamin nukiliya ga Iran da Koriya Ta Arewa da Libya.
Bayan ya amsa laifinsa a gidan talabijin na ƙasa, shugaban ƙasar na wancan lokacin Pervez Musharraf ya yafe wa masanin amma kuma ya ci gaba da zama cikin ɗaurin talala tsawon shekaru.