Tsere wa Mulkin Taliban: An yi wa ‘Yan ƙwallon Mata Tayin Komawa Birtaniya
Matasan ƴan ƙwallon Afganistan mata, waɗanda suka tsere daga Taliban, an yi ma su tayin cewa za su iya zuwa Birtaniya tare da iyalansu.
Mambobin 35 daga tawagar matasan ƴan ƙwallo ne suka tsere daga Kabul a watan da ya gabata kuma suna zauna ne a otal a Pakistan tsawon makwannin da suka gabata.
Ofishin harakokin cikin gida na Birtaniya ya ce yana aiki don kammala aikin ba su bizar kuma yana fatan yin maraba da su zuwa Birtaniya nan ba da jimawa ba.
Birtaniya za ta karɓe su ne tare da iyalinsu.
Gidauniyar ROKiT, wacce ta goyi bayan tserewarsu daga Afghanistan, ta ce matasan ƴan ƙwallon sun yi farin ciki da aka ba su damar a rayuwarsu.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here