Buhari ne Kawai Wanda Zai Iya Zuwa ko Ina Mutane su Taru ba Tare da ya Nemi su ba – Osinbajo
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce Najeriya za ta yi nasarar magance dukkanin matsalolin da ke addabatarta tare da cewa farin jinin Buhari ne zai yi tasiri ga magance ƙalubalen ƙasar.
Osinbanjo ya bayyana hakan ne a wani zaman tattaunawa da ya yi da manyan jami’an ofishin jekadancin Najeriya a Birtaniya a ranar Asabar.
“Shugaban kasa watakila shi ne ɗan siyasar Najeriya mafi shahara da muka taɓa yi a zamani da dama,” in ji Osinbajo.
Mataimakin shugaban na Najeriya ya ce Buhari ne kawai wanda zai iya zuwa ko ina mutane su taru ba tare da ya nemi su ba.
Ya ce abin da Najeriya take buƙata kenan domin magance matsalolinta. “Ina tunanin saboda girman amincinsa, har yanzu shi kaɗai ne zai iya kiran kowa, har mutanen da ba su yi amanna da shi ba sun san cewa mutum ne mai tsaya wa kan kalamansa.”
Ya jaddada haɗin kan Najeriya inda ya ce wurare da dama a duniya na ƙoƙarin haɗa kai ta la’akari da bunƙasar tattalin arziki amma ba rabuwa suke yi ba, “wannan ba lokacin ɓalle wa ba ne.”
Osinbanjo ya ce dukkanin ƙabilun ƙasar suna dogaro ne da juna, “idan ka dibi dukkaninmu da muke zaune a nan, mun fito ne daga shiyoyi daban-daban.
Ya ce Yarbawa da ƴan ƙabilar Igbo da Hausawa dukkaninsu ba za su ce sun wadatu su kaɗai ba, “Mun fi dacewa da ƙasa ɗaya, shi ya sa muke da karfi kuma shi ya sa za mu iya fuskantar duniya,” in ji shi.
Ya yi kira ga ƴan Najeriya na gida da mazauna ƙasashen su dinga yaɗa saƙwannin nuna kishin ƙasa ɗaya, yana mai cewa duk wanda ya kalli yadda Najeriya ke tafiya ya san cewa ta fi jin daɗin tafiya a tsarin da take, “kuma wannan ita ce gaskiya.”
Mataimakin shugaban wanda ya ce Najeriya na fuskantar ƙalubalen tsaro da na tattalin arziki, amma a cewarsa hakan na iya faruwa ga ko wace irin gwamnati kuma gwamnatinsu na kan hanyar magance matsalolin ƙasar.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here