Kisan Masu Zanga-Zanga: Kotu ta Tsare ɗan Minista
Wata kotu a arewacin Indiya ta garkame ɗan wani ministan gwamnati, wanda ake zargi da hannu a mutuwar manoma hudu yayin zanga -zanga makon da ya gabata a Uttar Pradesh.
Ashish Mishra, wanda aka kama da yammacin ranar Asabar, ana zarginsa da kutsawa cikin masu zanga-zangar da mota.
Ya musanta cewa yana cikin motar.
Bayan abin da ya faru masu zanga-zangar da suka fusata sun cinna wa motoci wuta inda kuma aka kashe mutum huɗu.
A ranar Juma’a kotun ƙoli ta ce ba ta gamsu da binciken ƴan sanda ba.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here