Katsina: Dakarun sojoji Sun Kashe Wasu ‘Yan Bindiga
Rundunar Operation Hadarin Daji ta samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 5 a karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina.
Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya sanar da hakan a Abuja, inda yace rundunar ta samu nasarar ceton mata 3 da yaransu.
Sai dai, daya daga cikin jaruman sojojin ya rasa ransa yayin kokarin ceton wata mata mai shayarwa, a cewar John Enenche Rundunar Operation Hadarin Daji sun ragargaji ‘yan bindiga 5, sun samu nasarar ceton mata 3 da yaransu a kauyen Diskuru da ke karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, Daily Nigerian ta ruwaito.
Read Also:
Manjo janar John Enenche, kakakin rundunar soji, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake bayar da jawabi a kan yadda sojojin arewa maso yamma da sauran wurare a Najeriya suke tafiyar da ayyukansu tsakanin ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 4 ga watan Nuwamba
. “Sai dai wani jarumin soja ya rasa rayuwarsa wurin kokarin ceto wata mata mai shayarwa,” cewar Enenche.
Enenche ya ce rundunar ta samu nasarar kama wasu mutane 2 da ake zargin sun hada kai da wasu ‘yan ta’adda da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, da wasu ‘yan ta’adda 2 da ke karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.
“Ga dukkan alamu, sojojin Najeriya na iyakar kokarin ganin sun kawo karshen ta’addanci a Najeriya,” a cewarsa.
Enenche ya ce ba kashe ‘yan ta’addan kadai rundunar sojin take yi ba, ta samu nasarar amsar miyagun makamai da dama daga hannunsu.