Dakta Mohammed Junaid ya Caccaki Buhari da Jam’iyar APC

Batun kisan manoma 43, da mayakan kungiyar Boko Haram suka yanka, ya tayar da hankulan jama’a.

Jama’a da dama, musamman ‘yan arewa, sun mamaye dandalin sada zumunta da alhinin kisan manoman.

Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za’a taba samun zaman lafiya a Najeriya matukar APC da Buhari su na kan mulki.

Tsohon dan majalisa a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za’a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki.

A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a ranar Asabar.

“Na san ya zuwa yanzu ‘yan Najeriya sun gaji da labaran kisan fararen hula a yankin arewa maso gabas, musamman a jihar Borno.

“Yanzu kuma babu sauran dan Najeriya da bai yarda cewa akwai ‘yan bindiga da ke kashe mutane a arewa maso yamma, musamman jihar Zamfara, Katsina, Sokoto, da Kaduna ba.

“To babu amfani a wurin wannan lusarar gwamnati ta ke aika sakon jaje duk lokacin da ‘yan ta’adda suka kashe mutane, ya kamata a ce an wuce wurin da zasu ke fitowa suna cewa kisan fararen hula ya girgizasu.

“Duk abin da ya ke faruwa, ya na faruwa ne saboda babu gwamnati a kasar nan.

“Matukar dai Buhari da APC za su cigaba da zama a gwamnati, ba za’a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba, mulkin Najeriya ya fi karfinsa, ba zai iya ba.

“Ya fadi kasa warwas, amma saboda munfurci irin na ‘yan Najeriya, da kabilanci, da nuna bangaranci, da siyasar addini, wasu gani suke Buhari ya na tabuka wani kirki.

“Bai tabuka komai ba Kuma babu abinda zai iya yi, idan ‘yan Najeriya suna son ganin canji sai su yi wani abu ko kuma su yi shiru, su daina korafi,” a cewar Dakta Junaid.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here