Garkuwa da Mutane a Titin Abuja – Kaduna ya Zama Ruwan Dare – Umar Mohammad
Tsokacin Edita: Dukkan abubuwan da zasu karanta a wannan rubutu ra’ayin marubucin ne ba ra’ayi Legit.ng Hausa ba.
Murna dai ya koma ciki musamman ga matafiya dake sintirin bin titin Kaduna zuwa Abuja ganin yadda hare-hare da garkuwa da mutane ya dawo sabo fil a wannan titi.
A cikin makonni biyu zuwa uku da duka wuce kusan duk kwana daya zuwa biyu sai kaji mahara sun dira hanyar sun kwashe mutane kamar awakai.
A kwanakin baya dai musamman a lokacin Korona, abin ya dan yi sauki domin mutane da dama dun koma bin titin gadan-gadan, sai dai ashe miyagun mutanen likimo suka yi suna jiran wani lokaci su koma sana’a.
Wannan matsala na garkuwa da mutane a Najeriya musamman a Arewacin Najeriya ya zama ruwan dare. Tsoho, yaro kai har jariri bai tsira ba daga hannun wadannan mutane.
Read Also:
Shiga babban birnin tarayya, Abuja, ya zama abin tashin hankali a kasar nan musamman idan daga Arewa kake.
Idan kafito da ga Sokoto, Gusau ne tun daga can zuciyar ka zai yi ta harbi har sai iso Kaduna, daga Kadunan ma wata sabuwar tashin hankali ne idan ka fara sallama da gwanin gora.
Mutumin Katsina ma tun daga can cikin fargaba da tashin hankali ya ke biyo wannan hanya, babban tashin hankalin shine ka samu ka tsallake siradin daga Olam zuwa Zuba, Kai jama’a Ina zamu je na Ƴan Arewa?
Kilomita duka-duka bai wuce 180 daga Kaduna zuwa Abuja haka daga Abuja Zuwa Kaduna amma kiri-kiri an kasa kawo karshen sa.
A kwashi mutane, ayi cinikin su kamar bayi amma kasa kamar babu jami’an tsaro. Suma shugabannin sun sadakar, sai dai su bi jirgin kasa talaka kuma ko oho.
Direbobi da dama sun ce sai su taso tun daga Maiduguri ko kuma Legas amma hankalin su baya ta shi sai sun hau titin Abuja zuwa Kaduna saboda tsananin rashin tsaro da tabbas.
Tsakani da Allah ace wai gwamnati ta kasa kawo karshen wannan masifa da mutane suka fada duka da madafan iko da ke hannun ta.
Rokon mu shine Allah ya kawo mana dauki ya kawo karshen wannan masifa da ya afka mana a musamman yankin Arewa.