Matsin Tattalin Arzikin Najeriya ba na Din-din-din Bane – Ministar Kudi

Ministar kudi ta kasa, Zainab Ahmed ta bayyana cewa matsin tattalin arziki da Najeriya ta shiga na dan lokaci ne.

Zainab ta sanar da hakan ne a taron tattalin arziki da ke gudana a Abuja a yau Litinin, 23 ga watan Nuwamba.

A ranar Asabar ne alkallumar kiddigar abinda kasa ke samu suka nuna cewa Najeriya ta sake shiga matsin tatallin arziki a hukumance.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa karayar tattalin arziki da Najeriya ta fada ciki a yanzu ba zai dauki dogon lokaci ba.

Ministar kudi da tsare-tsare ta kasa, Misis Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, a taron tattalin arziki karo na 26 wanda aka fara a babbar birnin tarayya, Abuja.

Ta ce: “Karayar tattalin arziki da aka fada ciki zai kasance na dan kankanin lokaci ne kuma masu ruwa da tsaki sun fara aiki tare domin samar da matakan da za su magance tare da inganta lamarin.”

Hukumar kididdiga ta kasa ta sanar da cewar Najeriya ta sake fadawa a matsalin tattalin arziki a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba.

Taron Tattalin Arzikin Kasa karo na 26, an shirya shi ne da hadin guiwar Ma’aikatar kudi, kasafi da tsarin kasa (FMFBNP), jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Taron zai ba masu ruwa da tsaki a gwamnati da kamfanoni damar yin nazari tare da kawo mafita ga halin da aka tsinci kai, musamman yadda annobar COVID-19 ta yi tasiri ga tattalin arzikin Najeriya.

A cewar rahoton kiddidigar abinda kasar ke samarwa a shekara, GDP, ta Hukumar Kididdiga na Kasa, NBS, ta fitar a ranar Asabar, hada-hadar kasuwanci sun ragu da kashi 3.62 cikin 100 a watanni uku na karshen 2020.

Wannan shine karo na biyu da GDP din ke raguwa a jere tun matsin tattalin arzikin da kasar ta fada a shekarar 2016.

Jumullan GDP din na watanni tara na farkon shekarar 2020 sun nuna alkallumar na -2.48%.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here