Daga Mansur Ahmed

“An ci zarafin yaran nan kuma Allah zai saka musu amma a shawarance, Maimakon wannan abinda ake kawai a bawa GANDUJE Qur’ani bugun Lawi Dan Zarga ka rantse da Allah cewar sharri akai maka”

Duk mutum mai cikakken imani wajibi yayi takaicin cin mutuncin k’ananan yaran da aka yi yau a jihar Kano da sunan kare mutuncin Gwamna Ganduje, na zubar da hawaye Ina zaune ni kad’ai jimawa a filin jirgin saman Nnamdi azikiwe saboda zafin wannan cin zarafin, maimakon ace suna aji suna daukar darasi tunda ranar karatu ce amma sai gasu ana Jagaliya dasu.

Yaran da wani a cikinsu ma idan ka tambaye shi waye Gwamnan Kano bai sani ba, balle yasan ma me ake nufi da gwamna ko meye aikin gwamna balle har yasan yadda akai Ganduje ya bayar da kwangilar aiki har ake zargin ya karb’i toshiyar baki, kuma duk cikin yaran nan babu wadda zaka nunawa bidiyonnwajen Jaafar kace masa wannan mutumin me ake bashi yake sakawa a aljihu bai ce maka kudi bane, amma saboda cin zarafin rayuwarsu da wulakanci aka debo su aka basu kwali suna d’agawa.

Abin ciwon ma ba ‘yan makarantar First lady collage ko Governors Collage bane balle ace ‘yan gata ne, yan makarantar kowa da kowa ne, kuma a cikin su banga alamar ‘ya’yan Gandujen ko ‘yayan Gawuna, ko ‘yayan Kwamishinan Ilmi ba, kai ko ‘yayan shugaban jam’iyyar APCn Kano da ake cewa bai yi karatun bokon ba ni ban gani ba haka kawai an debo ‘ya’yan talakawa ana wulak’anta gobensu dan ana son a binne rashin gaskiya.

Ita gaskiya sunanta gaskiya kuma duk abinda za’ayi mata dole ne sai ta bayyana kanta sunanta gaskiya dan haka ku dena b’ata lokacinku wajen b’oye ta, maimakon wannan cin zarafin ‘yaran a shawarance me zai hana Ganduje zuwa masallacin Sarki bayan kammala sallar juma’a a bashi Qur’ani bugun gwani Lawi Dan Zarga ya rantse da Allah cewar bai karb’i toshiyar bakin ba kuma yace Jaafar sharri yayi masa kamar yadda Jaafar din ya zo da nasa.

Wallahi da ace akwai d’an uwana a wannan daliban sai na shigar da k’ara kotu, Allah wadaran wannan abinda aka yiwa yaran nan kuma Allah ya saka musu.

 

The post Gwamna Ganduje bai kyautawa ‘Yan makaranta da aka fito da su tituna ba appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here