Daga Mahmud Isa Yola

Gwamnan jihar Adamawa, Umaru Jibirilla Bindow ya bayyana cewa zai kalubalanci Ahmadu Umuaru Fintiri, dan takarar Jam’iyyar PDP da ya lashe zaben gwamna a jihar Adamawa. Wannan yana zuwa ne makonni da Bindow ya taya Fintiri murnan lashe zabe, kana kuma ya nuna amincewar sa da sakamakon ba tare da zuwa kotu ba.

Bindow ya bayyana aniyar sa na kalubalantar PDP ne a wani taron manema labaru da yayi a Yola, inda sakataren kungiyar yakin neman zaben sa, Umar Duhu ya wakilce shi.

Bindow yace duk da cewa a baya yayi amanna da sakamakon zaben, bayanai da suka tattara ya nuna musu cewa akwai magudi da aka tafka a yayin gudanar da zaben a kananan hukumomi bakwai. Saboda haka, yace zasu kalubalanci nasarar Fintiri a kotu, inda a cewar sa, suna fatan a sake zaben ko a bayyana Bindow a matsayin wanda ya ci zabe.

Kazalika ya kalubalanci wasu wadanda a cewar sa ‘yan gidan shugaba Muhammadu Buhari ne inda yace sun hada kai da ‘yan jam’iyyar PDP a jihar.

“Zan iya gaya maka taron da matar shugaban kasa ta kira a Yola, an yi shi ne don tabbatar wa dan takarar PDP nasarar da ya samu a zaben.”

Har ila yau, Gwamnan ya nemi shugaban kasa Bubari da ya dakatar da wadanda ya kira masu yiwa jam’iyyar APC zagon kasa a jihar ta Adamawa.

The post Gwamnan Adamawa Bindow zai kalubalanci nasarar Fintiri a kotu appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here