Majalisar Dattijai ta Bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Fitar da N300b Don Gyara Hanyoyin Jahar Neja
Majalisar dattijai a ranar Talata ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da Naira biliyan 300 a matsayin kudin taimakon gaggawa don gyara munanan hanyoyi a jahar Neja.
Read Also:
Wannan kuduri na babban zauren ya biyo bayan wani kudiri kan lalacewar hanyoyi a fadin jahar Neja da toshe hanyoyin ta hanyar nuna rashin amincewa da direbobin tirela da direbobin tanka suke yi a cikin kwanaki hudu da suka gabata.
Mataimakin Babban Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Sabi Abudullahi, mai wakiltar Neja ta Arewa ne ya kawo kudirin, in ji rahoton The Nation.
A cikin gudunmawarsa, Sanata Mohammed Sani Musa, ya zargi Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola, da nuna son kai a aikinsa na gina hanyoyi da gyaran hanyoyi a jahar Neja.
Karin bayani na nan tafe…