Haihuwa da Yawa ba Gidadanchi ba ne, Tara su Barkatai Babu Tarbiyya Shi ne Ganganci da Cutarwa – Bello Shehu Maude

Ita haihuwa arziki ce, kuma ni’ima ce da Allah Ya ke bawa mutane a duk lokacin da Ya so.

Ba daidai bane cin mutunci, ko zagin wanda ya haifi yara da yawa idan har yana tarbiyantar da yaransa ta hanyar da ya dace.

Manzon Allah (SAW) Yana cewa Ku yi aure, ku hayayyafa, zan yi alfahari da ku ranar tashi alƙiyama.

A wani wajen kuma Manzo SAW yana cewa dukkanin ku masu kiwo ne, lallai za a tambaye ku kiwon da aka baku ranar tashin alkiyama

Sannan kuma a cikin Al-Ƙur’ani Mai Girma Suratul Isra’i Aya ta 31 Allah SWT yana cewa, “Kuma kada ku kashe ‘ya’yanku domin tsoron talauci, Mu ne ke arzuta su, su da ku. Lalle ne kashe su ya kasance kuskure babba.” (Q17:31)

Tsarin iyali ba laifi bane, ya samo asali a cikin addinin Musulunci domin ya zo a Hadisi cewa Sahabban Annabi SAW suna yin Azlu a lokacin Ma’aki SAW, kuma da labari ya je masa akan hakan bai hana su yi ba domin neman lafiyar iyalansu ta hanyar tazarar haihuwa.

Tsarin Iyali na zamani da ake yi a asibitocinmu bai ci karo da addininmu ba ko al’ada, shi ma yana tafiya ne da tallafawa mata iyayenmu domin inganta lafiyarsu data ‘ya’yansu a zamanance.

Tsarin iyali ba laifi bane kwata-kwata idan da yardar miji da matarsa saboda muhimmancin bayar da tazarar haihuwa ga lafiyar mace domin kare ta daga duk wata cutarwa ta sanadiyyar ciki da goyo da kuma kula da tarbiyyar yaro kafin wani juna-biyun ya ƙara shiga.

Babu wanda zai hana ka haifo yara, domin kuwa kowa da arzikinsa yake zuwa duniya. Amma ɗan uwa, ka yi duba zuwa ga lafiyar matarka da kuma irin dawainiyar da take sha lokacin renon ciki da kuma goyonsa har zuwa shayarwa. Na tabbata, hutu kafin wata ɗawainiyar makamanciyyar wannan shi ya fi muhimmanci domin kulawa da lafiyar ɗanka da kuma tarbiyyarsa kafin wani kuma ya ƙara zuwa daga baya.

Lafiya ita ce uwar jiki, wacce babu ɗan adam da zai yi fushi da ita ko kuma ya fara ganganci da ita. Haihuwa shekara bayan shekara ga ‘ya mace ganganci ne da lafiyarta domin haihuwa akai-akai na rage mata ƙarfin jiki da kuma jawo naƙasu ga yaron da take goyo domin bai samu isasshen kulawa ta shayarwa ba, ballantana jikinsa yayi kwarin da ya kamata.

Yawan haihuwa bashi da alaƙa da talauci na dukiya ko kusa. Allah Ya kan azurta mutum da haihuwa kuma ya azurta shi da dukiya mai yalwa sannan kuma ya sanya tarbiyya ta kirki a cikin zuri’ar. Za’a kuma a iya samun akasin hakan, su zuma zuri’ar da zasu buwayi al’umma waɗanda ko kusa basa daga cikin waɗanda Annabin Rahama zai yi alfahari da su a ranar alkiyama.

Zaka iya haifar yaro guda ɗaya tilo a tsawon rayuwarka, idan baka tarbiyantar da shi ba, ya buwayi duniya. Fir’auna shi kaɗai mahaifansa suka haifa, amma sai da ya fitini duniya har yayi ikirarin shi Allah ne mafi girman laifi a duniya.

Mu gane cewa gorantawa ko kuma izgili ga wanda ya haifo yara barkatai kuma Allah bai hore masa arzikin da zai kula da su ba, har suka zama marasa tarbiyya ba shi ne zai gyara mana yawan hayayyafar da mutane ke yi ba-kan-gado ba. Mu yi nuni ga illar da take faruwa da iyayenmu mata wajen haihuwa ta yadda wata ma yawan hakan kan iya jawo sanadiyyar ran ta, sannan kuma mu yi nuni ga rashin kula da yara ke fuskanta har ta kai su ga sun rasa tarbiyya ta gari wanda babu yaron da shi a sonsa zai zama mara amfani a cikin al’umma.

Mu rage tsangwama ko cin fuska da cin zarafin duk wani wanda ya tsinci kansa a cikin gidan yawa, domin babu wanda akai shawara da shi kafin ya zo duniya. Idan ka ganka a cikin rayuwa mai kyau ba wayonka ko dabarar ka ba ce ta baka, idan kana cikin ƙuncin rayuwa ba tsanarka Allah Yayi ba. Komai akwai sanadi da kuma sila a rayuwa.

Allah Ya taimake mu, mu kula da lafiyar ‘ya’ya mata musamman wajen haihuwa domin rayukansu na salwanta idan akayi ganganci.

Bello Shehu Maude
Ya rubuta daga Kano

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here