Daga Malam Aminu Gandi

Jihar mu ta Sokoto na da alamun fuskatar muguwar barazanar rashin tsaro nan bada dadewa ba. Lallai duk abinda muke gani a halin yanzu wargin yara na in aka hango abinda ke kan hanya taso ma Sokoton.
Bayan ta’addancin da wasu ‘yan siyasa ke haddasawa ta hanyar diyan talakawan cikin gari (Area Boys) to babbar barazana mai tashin hankali itace ta Barayin Shanu masu garkuwa da mutane.

Cikin satin da ya gabata Gwannan Zamfara ya amince da kafa kungiyar tsaron ‘yan sa kai wadda zata hwara da jama’a 8,500 saboda magance matsalar tsaron da ke addabar su. Wannan abin farin ciki ne sosai ga jama’ar Zamfara da Sokoton, to amma kuma abin tashin hankali ga Sokoto da Mutanen Sokoton saboda tabbas Barayin Shanun nan da Masu garkuwa da mutanen ba inda zasu sake kafa wata tashar ta’addanci in ba dazukan yankin Sokoto ba.

Munga misalin hakan a lokacin da Soja suka fatattake su ‘yan watannin da suka gabata. Don haka ya zama wajibi a zauna da gaugawa don daukar matakin hana kwararowar wadan nan miyagun cikin yankin Na Jihar Sokoto.

Yanzu haka mutane da yawa Na zaman dar dar musamman mutanen yankin Isa, Sabon Birni, Rabah, Tureta, Dange Shuni, Tangaza da Gudu saboda bayyanar wadan nan mutanen da ayukkan su a wadannan yankunan.

Kadan daga cikin Matakan da muke ba Gwannatin Sokoto shawarar ta dauka saboda magance matsalar sun hada da;

1. Gwamnan Sokoton don Allah don son Manzo ya dawo gida Ya zauna, ya sassauta ma kainai yawon ga haka nan; duk da yake wani yazo muna da wata maganar mata wai “Wai Magani ankayi ma Gwamna Tambuwal din da Farfesun dwagin Kare da hikahikan kolo” don ya kama shekawa shina tashi sama. To tunda an gane missa ba’a kare makarun?

2. Gwamnan ya gaggauta zama na tsakani da Allah tare da Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi tare da duk uwayen kasa Na jihar Sakwkwaton baki daya, don a samu shawara ta bai daya da kuma mataki na bai daya. Sarakunan mu na Musulunci sun san kowa kuma sun san ko wane lungu na gundumomin su, sa’annan suna da Zarumman mazaje da zasu saka gaba don magance ayukkan ta’addanci. Bugu da qari a inganta abashin Sarakuna da Hakimman su, saboda su sami kudin aiki da na abin masarufi. Tabbas amfanin Sarakuna ga Al’umma yafi na na ‘yan siyasa musamman wurin wanzan da zaman lafiya da tsaro.

3. Gwamnatin Sokoto ta gaggauta kafa Kungiyar Tsaro ta ‘Yan sa kai daga kowace Masarauta dake jihar Sakwkwaton wadda zata kunshi aqallan mutum dari biyar biyar daga kowacce Masarautar wadan da zasuyi aiki tare da jami’an tsaro karkashin kulawar Mai Alfarma Sarkin Musulmi don magance wadan nan ‘Yan ta’addan da ke neman yi ma jihar Sakwkwaton mugun kutce da fyde.

4. Muna da labari daga majiya mai inganci cewa Gwamnatin jihar Sakwkwaton ta bayar da aikin sawo Mashuna aqalla guda 1,000 daga kasar China wanda wani jami’in Gwamnatin da aka tura yanzu haka a sanina yana China din don sawo baburan. Wannan ci gaba ne, amma na mai shiga Rijiya. Don ina tabbatar da cewa galibin wadan da za’a raba ma baburan nan zasu sayar da su ne, kuma a karshe in ba’ayi hankali ba wadan nan ‘yan ta’addar sune zasu saye baburan don suna da kudi hannun su. Kuma wadannan baburan sune mafi alfanun abin hawa ga miyagun, wanda in babu su to ayukkan nasu na ta’addaci zai gurgunta matuka. Nayi rubutu watannin baya na ya kamata Gwamnati ta dauki matakin hana amfani da manyan mashinan nan masu karfi saboda dasu ake ta’addacin gari da na daji. To amma sai gashi wai Gwamnati da kanta ke bayar da kudi a sawo wadan nan makaman da zasu kashe Al’umma.

5. Ya kamata Gwamnatin Sakwkwato ta tashi tsaye don yakar mugun talauchin da Al’umma ke ciki ta hanyar sakin mara ga kananan hukumomi don su iya gudanar da ayukkan raya kasa da kansu ba tare da mugun shishigin Ministry for Local Government ba. Wanda hakan zai ya ba shuwagabannin kanan hukumomi damar magance matsalar tsaro a matakin farko.

6. Don Allah Gwamna ya dawo ya zauna yayi ma mutane aikin da suka zabe shi yayi musu. Duk bobawan da Ke son ganin Gwamnan to yazo ya cimmai Sokoto.

7. Don Allah Gwamna Ya dawo Sokoto Ya zauna yayi ma mutanen da suka zabe shi adalchi wanda ko don ganin idon shi za’a yi abin kirki.

8. Don Allah Gwamna Aminu Waziri ya dawo Gida ya zauna don ban san minana yakayi Abuja ba da yafi amanar mutane da ya dauka ba.

9. Don Allah Gwamna Aminu Waziri ya dawo gida ya zauna saboda shi at Gwamna yanzu, in har yawo yaka son ya tafi to ya bari sai ya sauka ko kuma in ya fadi zabe.

10. Don Allah Magaji Ka dawo gida Ka zauna ko don gyaran siyasar Ka, Wallahi Ina ganin kila Don baka taba faduwa zabe ba shi yassa kaka wasa da rayuwar mabiyan Ka. Mu tsoffin ‘Yan DPP mun san wulakancin faduwa zabe. Ina ganar maka hatsari tafe in baka gyara ba. Wallahi magoya bayan Ka suna kuka da kai, kuma kullum bakin ciki kaka sa su. Mu iyakar mu da ku kallo sai ko dariya in kun fadi zabe.

Daga karshe muna rokon Gwamnati da sauran jami’an Gwamnati da sauran ‘yan siyasa masu bata tarbiyar yaran mu na cikin gari ta hanyar saka su cikin harakar ta’addaci na Area Boys da su ji tsoron Allah. Wallahi duk wanda ya bata Dan wani to lallai sima nashi ‘Dan bai tcira don Allah baya zalunci. Bashi yiwuwa kun baro naku ‘yan uwa kauyukkan ku ku taho cikin gari ku bata muna namu ‘yan uwan saboda biyan bukatun ku.

 

The post Hattara Gwamna Tambuwal, Sakkwato na fuskantar matsalar tsaro appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here