Daga Aliyu Muhd Sani

Wani abu da ya kamata mutane da hukumomi da kungiyoyin kare hakkin bil’adama su sani game da ‘Yan Shi’a da suke fada da Gomnatin Nigeria shi ne; asali tafarkin Shi’a ya ginu ne a kan neman mulki, wato a kan Aqidar Imama. Wannan ya sa tun farkonsu da yaki da Gomnati aka sansu, kuma ba za su dena ba har abada. Saboda Aqidarsu ta Addini ta ginu ne a kan neman mulki, in kuwa mulki ba a hanunsu yake ba to sai sun yaki kowace Gomnati. Saboda suna da Aqidar cewa; a yanzu haka ana karkashin Imamancin Mahdi ne, wanda ya shiga gaiba (ya buya), wanda nan gaba suna sa ran fitowarsa da bayyanarsa.

Haka lamarin Shi’a ya kasance a tsawon Tarihi. Har zuwa wannan zamani da Khomeini ya ci nasarar kafa Gomnatin Shi’anci a Iran, a karkashin Nazariyyar “Wilayatul Faqeeh”, wato shugabancin wakilin Mahdi. Kuma ita wannar Gomnati ta Khomeini mai wannar Nazariyya, tana bin tafarki ne na “Juyin juya hali” (Thaura/ Revolution), wato Gwagwarmayar kifar da Gomnatoci a kafa Gomnatocin Shi’anci masu bin Nazariyyar “Wilayatul Faqeeh” a gurbinsu. Wannan juyin juya hali ya ci nasara a Iran a shekarar 1979, kuma suka dauri aniyar jefa wannan juyin juya hali zuwa ga sauran kasashen Duniya, ta yadda kafin bayyanar Mahdi an gama kafa masa Gomnatoci a kasashen Musulmai gaba daya.

Wannan tsari na “Juyin juya hali” (Thaura/ Revolution) sun kafa masa ginshikai a kusan dukkan kasashen Musulmi, tun daga kasashen Larabawa musamman Iraq, Lebanon da Yemen, har zuwa kasashen Afirka, musamman Nigeria, Niger, Ghana da Tanzania da sauran inda suka samu dama.

To in an lura za a ga yadda ita wannar harka ta juyin juya hali ta yi karfi a Lebanon da Iraq da Yemen, inda a Iraqi suke da kungiyoyi masu yawa, a Lebanon suke da kungiyar Hizbullah wacce take da rundunar soja da take yaki a kasa da kasa. Haka a Yemen suke da kungiyar Hutsawa (Houthis), wanda a halin yanzu suke gabza bata-kashi da kawance kasashe karkashin jagorancin Saudiyya, saboda yunkurin juyin mulki da kwace Gomnati da suka yi a Yemen din.

Haka kuma in an lura da kyau za a ga cewa; salon da Kungiyar Hizbullah ta Lebanon take bi na kokarin kwace Gomnati irinsa ne babu banbanci ‘Yan Shi’a mabiya Zakzaky suke bi a Nigeria. Kuma za a ga irin maganganu da furuci da jawabai da Hassan Nasrallah yake yi irinsu ne Zakzaky yake yi, na nuna isa, da nuna sun fi karfin Gomnati, da nuna cewa; a kowane lokaci za su iya kwace Gomnati.

To da wannar ‘yar takaitacciyar matashiya nake jan hankalin masu ruduwa da tarzoma da ‘Yan Shi’ar suke yi, cewa; ya kamata su sani; ko an kashe ‘Yan Shi’a a Abuja, ko ba a kashe su ba, ko an kashe su a Zaria, ko ba a kashe su ba, ko an kama Zakzaky ko ba a kama shi ba, to shirinsu shi ne; dole sai sun kifar da Gomnatin Nigeria, sun kafa Gomnatin Shi’anci bisa wancan tsari na Gomnatin Iran ta “Wilayatul Faqeeh”, wannan ya sa suke kiran Zakzaky da sunan: Wakilin Mahdi. Wato wanda zai kafa wa Mahdi Gomnati a Nigeria.

Don haka wanda bai san manufarsu ba sai ya sani. Kuma wannan ba ya bukatar kawo shaida, saboda kowa ya san irin furucin Zakzaky da mabiyansa a kan Gomnati da jami’an tsaro. Don haka a kwana da shirin cewa; manufar wadannan ita ce: kwace Gomnatin Nigeria da kafa Gomnati mai nuna goyon baya ga Iran, a karkashin jagorancin Zakzaky ko magajinsa.

 

The post Rikicin Shia da Gwamnati: Mafari da manufa appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here