IGP ya Bada Umarnin Gudanar da Bincike Akan ‘Yar Wasan Dirama #Rahma Sadau

Duk da bidiyo da hirar da tayi, ana tsoron kalaman batanci da hotunan Rahada Sadau ya haifar ka iya haddasa fitina.

Tsoron haka IGP Adamu ya bada umurnin gudanar da bincike cikin gaggawa Sifeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya bada umurnin gudanar da bincike kan ‘yar wasar dirama, Rahama Sadau, kan cece-kucen da ya biyo bayan hotunan tsiraicin da ta wallafa kan dandalin sada zumunta.

‘Yar wasan diraman ta daura wasu hotuna kuma hakan ya haddasa kalaman batanci ga manzon Allah (SAW). Daga baya Rahama ta bada hakuri kuma ta goge hotunan da ta daura.

Hakazalika ta barranta kanta da kalaman batancin. Mujjarlar wasar kwaikwayon Kannywood, Mujallar FIM, a ranar Asabar ta ruwaito cewa ‘yar wasan ta dakatad da tafiya birnin Dubai da ta shirya yi domin amsa sammacin yan sanda a Kaduna.

Mujjalar ta ruwaito cewa da an damke ‘yar wasan a Abuja amma wani babban jami’in yan sanda ya roki abokan aikinsa su daga mata kafa ta amsa sammaci a kaduna.

A wasikar babban hadimin IGP ya aikewa kwamishanan yan sandan jihar Kaduna, ya bukaceshi yayi abinda ya kamata domin tabbatar da cewa abinda tayi bai haifar da rikici ba.

“Ina mai aika maka umurnin Sifeto Janar na yan sanda cewa ka dauki matakin da ya dace wajen tabbatar da cewa wannan abu bai haifar da wani rikici ko tashin hankali ba.”

“Sifeto Janar na yan sanda na baka umurnin cewa ka aiko masa rahoton yadda abin ya kasance,” DCP Idowu ya rubuta a wasikan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here