Jawabin Buhari na Ranar Alhamis ya Bar Baya da ƙura
Bayanin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi a ranar Alhamis ya bar baya da ƙura, inda jama’a da dama ke zaton shugaban zai taɓo wasu batutuwa amma ya yi biris da su.
Wannan ne karo na farko da shugaban ya yi muhimmin jawabi sau uku ciki wata guda, inda ya yi a ranar 1 ga watan Oktoba da 12 da kuma 22.
A jawabin da ya yi na ranar Alhamis, shugaban ya gargaɗi masu zanga-zangar #EndSars da su daina zanga-zangar sakamakon gwamnatin ta saurare su, tare da jan kunnen waɗanda suka ƙwace ragamar zanga-zangar suka mayar da ita wata fafutuka ta daban.
A baya dai wasu daga cikin manyan tsoffin shugabanni da ‘yan gwagwarmaya da manyan mutane daga ƙasashen waje sun caccaki shugaban kan ƙin fitowa ya yi magana a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar barazana daban-daban.
Wani ɗan jarida ɗan Najeriya mazaunin Amurka Farooq Kperogi, ya wallafa a shafin Twitter cewa jawabin na Shugaba Buhari bai taɓo abubuwa kamar kashe-kashen da aka yi a Lekki ba da kuma mutane da dama da aka kashe a ƙauyen Tungar kwana da ke Talatar-Mafara a jihar Zamfara.
Shi kuma Sanata Shehu Sani, wanda tsohon sanata ne da ya wakilci Kaduna Ta Tsakiya a Majalisar Dattawan ƙasar, ya yi shaguɓe ga ‘yan ƙasar inda yake cewa sun buƙaci shugaban ya yi musu jawabi kuma ya yi jawabin ga shi sun rasa abin faɗa.
Ita ma Jam’iyyar PDP, wadda ita ce babbar jam’iyyar adawa a ƙasar, ta nuna rashin gamsuwarta kan wannan jawabi na shugaban a shafin Twitter inda ta ce jawabin da aka jima ana jira abin takaici ne kuma ya sha bamban da abin da aka so a ji ya faɗa.
Read Also:
EndSars: Buhari ya buƙaci ‘yan Najeriya su kwantar da hankalinsu
Clinton ta yi kira ga Buhari ya dakatar da kashe masu zanga-zangar EndSARS
Shin yaushe za a kawo ƙarshen zanga-zangar EndSars?
Me aka so ji daga bakin shugaban?
‘Yan ƙasar da dama sun yi zaton batun farko da shugaban zai fara yin magana a kai shi ne ya fito a jajanta wa mutanen Legas kan abin da ya faru a Lekki da kuma irin asarar da aka tafka.
A wata hira da BBC ta yi da wani ɗan jarida a Najeriya, Mannir Ɗan-Ali, ya bayyana cewa jagororin wannan zanga-zangar sun so su ji gwamnati ta yi musu lafazi mai taushi tare da bin su da lalama domin daina zanga-zangar.
Ya bayyana cewa “tun da suka latsa suka ga jini, ma’ana tun da gwamnati ta fara karyowa can a baya kafin ta yi shiru da abin har zuwa lokacin da Shugaba Buhari ya yi bayani, sai suke ganin Buhari zai fito ya yi magana akan harbe-harben da aka yi a Lekki wanda suke gani shi ne ya jawo lamarin ya rikice.”
Me shugaban ya fi mayar da hankali a kai a jawabinsa?
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince kan cewa ba shakka al’ummar kasar na da damar yin zanga-zanga kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya basu dama, sai dai sashen ya buƙaci a kiyaye doka a kuma kauce wa shiga hakkin jama’a.
A cewarsa, duk da sashe na 40 na kundin tsarin mulkin Najeriya da ya bai wa ‘yan kasa damar yin zanga-zanga, ya kuma yi gargaɗi a kan tayar da yamutsi da sunanta.
Shugaban ya kuma yi kira ga ‘yan kasar su koma harkokinsu, bisa alkawarin cewa jami’an tsaro za su ci gaba da ƙoƙarin kare lafiya da dukiyoyinsu musamman ‘yan sanda.
Ya kuma yi magana kan walwalar ‘yan sanda inda ya ce gwamnatinsa ta dauki matakai don tabbatar da walwalarsu, ta yadda za su kiyaye rayukan jama’a yadda ya kamata.
Ya kuma ce an bai wa hukumar kula da albashi umarnin sake nazartar albashin ‘yan sandan, har ma da sauran hukumomin da suka hadar da na hukumar kashe gobara.
Shugaban ya kuma bayyana cewa babu wata gwamnati a Najeriya da ta ɗauki gabarar yaƙi da talauci ta hanyar bijiro da matakai daban-daban na magance su kamar tasa, don haka ya kamata masu zanga-zangar su lura cewa da gaske suke wajen shawo kan matsalolin da suka shafi matasan Najeriya.