Home DUNIYA Legas: Yadda Wasu jama’a su ka Fasa Rumbun Ajiyar Kayan Tallafin Korona

Legas: Yadda Wasu jama’a su ka Fasa Rumbun Ajiyar Kayan Tallafin Korona

0

Legas: Yadda Wasu jama’a su ka Fasa Rumbun Ajiyar Kayan Tallafin Korona

 

    Tirmitsitsi ya barke a Lagos, yayin da cincirindon mutane su ka fasa wani sito da aka ajiye kayan tallafin korona su ka rika jidar kayan abinci, a Monkey Village da ke Maza-maza, cikin unguwar Odofin.

Kayayyakin da aka rika jida din dai duk an buga masu tambarin ‘COCAVID’, NOT FOR SALE; wato kayan tallafin korona ne, ba na sayarwa ba ne.

Kayayyakin sun hada da shinkafa, macaroni, taliya, gishir, garri, sukari da kuma katan-katan na indomi.

Wani mazaunin unguwar ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa tun safe mazauna unguwar ke ta jidar kayan abincin.

“Da farko dai wasu mutane ne su ka isa sito din da safe su ka dauki wasu kayayyakin abincin. Dama sun saba zuwa kowane lokaci su na kwasa.” Haka wani mazaunin unguwar wanda ya roki kada a bayyana sunan sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES.

“Lokacin da mutanen su ka lodi kayan abinci za su tafi, sai aka rika rokon su su bai wa wadanda ke wurin, amma su ka ki. Bayan sun tafi sai aka taru aka fasa sito din, kowa ya rika jida kawai. Gwamnati ta kimshe abinci, ba ta raba ba, ga kuma jama’a na cikin halin kunci.”

 

 

 

 

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest News
An Baiwa Fulani Wa'adin Barin Yankin su a Jihar KwaraKoci Iraola Zai bar BournemouthKotun ƙoli ta Sanya Rana Kan Shari'ar Jam'iyyar ADCMe Akpabio ya ce kan Rashin Tsaro?Yadda Aka Raba Mukaman Shugabancin ADC a Jihar KanoAmurka ta Sanya Takunkumin Hana Zirga-Zirga a Mashigar Hormuz Bayan Taƙaddama da IranLuguden Bam na Jirgin Yaƙi ya Kashe Mutane da Dama a Borno da Yobe2027: Ƙungiyoyi Sun Amince da Garba Yusuf a Matsayin Ɗan Takarar Majalisar Dattawan Kano Ta TsakiyaEFCC ta Roƙi Kotu da ta ƙwace Kadarorin MalamiKotu ta yi Watsi da ƙarar NBC kan Cin Tarar Gidajen Radiyo da Talbijin a NajeriyaƳan Bindiga sun Sace Mutane Sama da 150 a ZamfaraINEC ta yi Watsi da Buƙatar ADC kan Cire ShugabantaKamfanin Samar da Mai da Iskar Gas a Najeriya Sun Shiga Yajin AikYaƙin Iran: Kayan Abinci ya yi Tashin Gwauron Zabbi - MDDSojoji Sun Ceto Mutane 3 Daga Hannun 'Yan Ta'adda a Jihar Borno