Jiragen Yaƙi da Gwamnatin Najeriya ta Siya Daga Amurka 6 Sun Taho Najeriya

 

Rahotanni sun bayyana cewa jiragen yaƙi guda 6 ƙirar A-29 Super Tucano da Najeriya ta siya daga Amurka sun taho Najeriya.

Tun a watan Fabrairun 2018 ne gwamnatin Najeriya da siya jiragen guda 12 kan kudi dala miliyan $496m.

A watan Yuli, 2021, jirage 6 daga cikin 12 a rukunin farko suka iso ga rundunar sojojin saman Najeriya.

Abuja – Kashi na biyu na jiragen yaƙi guda 6 ƙirar ‘A-29 Super Tucano’ sun baro ƙasar Amurka, sun kamo hanyar zuwa Najeriya.

Mai taimakawa shugaban ƙasa ta ɓangaren yaɗa labarai, Tolu Ogunlesi, shine ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.

A wani rubuta da ya tura a shafinsa daga Telegram, Ogunlesi ya bayyana cewa jiragen yaƙin sun tsaya a Rectrix domin zuba musu mai zuwa Najeriya.

Yaushe zasu iso Najeriya?

Rahotanni sun nuna cewa ana tsammanin jiragen zasu dira a ƙasa Najeriya a tsakanin 24 ga watan Satumba da muke ciki.

Yace:

“Jiragen sun sauka a filin sauka da tashin jirage na Worcester Regional dake Rectrix domin duba lafiyarsu da kuma ƙara mai.”

“Rundunar sojojin sama sun jima suna amfani da jiragen yaƙi na A-29 Super Tucano wajen yaƙi da yan ta’adda.”

Ambasadan Amurka a Najeriya ta ziyarci matuƙa jirgin

Rahoto ya bayyana cewa ambasadan ƙasar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard, ta je mahaifarta Worcester domin halartar wani taro a makarantar Doherty Memorial High School.

Leonard ta ziyarci matuƙa jiragen yaƙin, waɗanda zasu taho da jiragen zuwa Najeriya domin ganin tashin su, ranar Alhamis.

Yaushe Najeriya ta siyo jiragen?

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta sayi jiragen yaƙi 12 na Super Tucano a kan kuɗi dala miliyan $496m tun a watan Fabrairun 2018.

Bugu da ƙari, kashi na farko na jiragen guda 6 sun iso ga rundunar sojojin sama a ranar Alhamis 22 ga watan Yuli.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here