Jami’an Tsaro Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane a Abuja
Rundunar ƴansandan Najeriya a Abuja, babban birnin ƙasar ta ce ta kama wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutanen ne domin neman kuɗin fansa a wani yanki na birnin.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun mai taimaka mata kan hulda da jama’a, Josephine Adeh, rundunar ta ce ta samu nasarar hakan ne a wani samame da ta kai a wani Otal da ke ƙauyen Bassa, bayan samun wasu bayanan sirri.
Read Also:
Abuja, babban birnin Najeriya na fuskantar matsalar tsaro a cikin watanni na baya-bayan nan.
Matsalar garkuwa da mutane da kashe-kashe na ƙara ƙamari, lamarin da ke janyo suka daga ɓangarori da dama.
Cikin sanarwar, rundunar ta bayyana sunan wasu matasa maza guda huɗu da mata biyu, waɗanda ta ce a cikin su akwai waɗanda suka yi ƙaurin suna wurin satar al’umma.
Sanarwar ta ƙara da cewa kayan da aka samu a hannun waɗanda aka kama sun haɗa da bindiga ƙirar AK47 guda ɗaya da wayoyin hannu 10 da kuɗi naira 345,000.