An Kama Sojoji 20 Masu Alaka da Boko Haram

 

Wasu sojoji da aka kama kan taimakon Boko Haram sun tona fararen hula da suke aiki da su.

Kimanin 20 da aka kama a Borno kuma yayin musu tambayoyi ne suka ambaci fafaren hulan da suka aiki tare suma an kamo su.

Amma Kakakin rundunar sojojin Nigeria, Mohammed Yerima ya ce ba shi da masaniya kan kama sojojin 20 da fararen hulan Wasu sojoji da aka kama yayin binciken masu daukan nauyin yan Boko Haram sun bayyana sunayen wasu fararen hula da suke aiki tare da su a cewar majiyoyi, rahoton Daily Trust.

An kama sojojin ne bayan bincike mai zurfi da aka yi kan alakar da ke tsakanin yan Boko Haram da jami’an sojoji, da suka taimaka musu wurin zagon kasa kan yakin da ake yi na kawo karshen ta’addanci a Nigeria.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da bincike kan wadanda suke daukan nauyin yan ta’adda da masu hada kai da Boko Haram.

Wani babban jami’in tsaro mai binciken sirri ne ka jagorantar binciken tare da babban janar na soja d wasu ma’aikata daga hukumomin binciken sirri.

Majiyoyi da dama sun sanar da majiyar Legit.ng cewa Hukumar Binciken Sirri na kasa, DIA tare da hadin kan DSS, NFU da babban bankin kasa CBN ne ke binciken.

A halin yanzu an kama sojoji 20 da ake zargi da hannu cikin lamarin kuma suna tsare a Borno. “An kama kimanin 20 daga cikinsu suna tsare a Borno.

A yayin binciken sun bada bayanai masu yawa ciki har da sunayen wasu fararen hula da suke aiki tare da su inda suka aka kama su,” majiya ta shaidawa Daily Trust.

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar sojoji, Manjo Jana Mohammed Yerima ya ce ba shi da masaniya kan kama sojoji da ake zargi suna hada kai da yan Boko Haram.

Ya kuma ce hukumar yan sandan farar hula, DSS, ya kamata a yi wa wannan tambayar domin su ke kula da batutuwan da suka shafi kama masu daukan nauyin ta’addanci.

Peter Afunanya, kakakin hukumar DSS, a yayin da aka tuntube shi a ranar Juma’a ya ce zai yi bincike kafin ya yi tsokaci kan batun.

Amma bai bada bayanin ba har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoton. Bai kuma amsa kira da sakon kar ta kwana da aka yi ta tura masa ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here