Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano ta Kama Mutane 14 da Aikata Fashi da Dabanci

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta sanar da kama mutum 14 waɗanda take zargi da aikata fashi da makami da tu’ammali da ƙwayoyi da kuma aikata dabanci a makon farko na watan azumin Ramadan.

Rundunar ta ce an samu nasarar kama mutanen ne a wani samamen da rundunarta ta dawo da zaman lafiya ta kaddamar.

Ta ce ta kuma ƙwato muggan maƙamai da haramtattun ƙwayoyi da kuma kayayyaki da aka sata.

A wata sanarwa da kakakin runduar ƴan sanda jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce kwamishinan ƴan sandan jihar, Mamman Dauda ya ayyana yaki kan duk wani nau’i na aikin dabanci a faɗin jihar.

Ƴan sandan sun ce suna iyaƙar kokarinsu wajen dakile dukkan ayyukan ɓata-gari a jihar.

CP Mamman Dauda ya gargaɗi duk masu aikata laifi da su guji yin hakan saboda za su iya fuskantar hukunci mai tsanani idan aka kama su.

Ya kuma bukaci al’umma da su kai rahoton duk wani abu da ba su yadda da shi ba, su kuma guji ɗaukar doka a hannunsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com