Denmark: An yi Garkuwa da Ma’aikatan Jirgin Ruwa Guda 16

 

Mamallakan jirgin ruwan ƙasar Denmark da masu fashi a teku suka ƙwace a mashigar Guinea a makon da ya gabata sun ce ƴan fashin sun tsere sun bar jirgin, inda suka tafi da ma’aikatansa guda 16.

Sai dai an samu nasarar kuɓutar da wasu da ke cikin jirgin mai suna Monjasa Reformer.

Waɗanda suka mallaki kwale-walen sun bayyana a ranar Talata cewa wasu ma’aikatan jirgin biyar sun samu mafaka a cikin wani ɗaki jirgin lokacin da ƴan fashin suka afka cikinsa.

Ƴan fashin sun ƙwace ikon jirgin ne a ɓangaren yammacin birnin Pointe-Noire da ke Jamhuriyar Kongo.

ahrefs guest posting

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com