Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa ‘Yan Najeriya Matsaloli 5

An shafe kusan mako guda kenan ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a Najeriya, kama daga bazuwar wanigurɓataccen man da ya dinga lalata ababen hawan mutane, zuwa samun dogwayen layuka a gidajen mai da kuma sayen man da matuƙar tsada.

Hukumomi dai tuni suka yi bayanin dalilan da suka sa aka samu yaɗuwar gurɓatacen man, wanda zuwa yanzu an dakatar da sayar da shi.

Amma har yanzu ba su bayar da wani bayani mai gamsarwa na dalilin da ya sa man yake wahala ba.

Sai dai kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce wannan rashin man da ake fama da shi a yanzu ya samu ne saboda killace miliyoyin litocin gurbataccen man da ya yadu a kasuwa.

BBC ta tambayi masu bin shafukanta na intanet kan su bayyana halin da arancin an fetur din ya saka su a ciki a yakuna daban-daban na Najeriya.

Kuma daga wallafa hakan a ranar Talata an samu bayanai daga kusan mutum 200 da suka bayar da labaran irin matsalolin da ƙarancin man fetur ya jawo wa ƴan Najeriya.

Bayan bin diddigin bayanan da aka turo, mun gano manyan matsaloli biyar da ƙarancin man ya jawo wa yan Najeriya.

1. Cunkoso a titunan da ke kusa da gidajen mai
Layukan a gidajen mai sun yi tsawo fiye da yadda aka saba gani a baya-bayan nan a manyan biranen Najeriya da suka haɗa da Abuja da Lagos, amma duk da haka gidajen mai ƙaɗan ne ke sayar da fetur din.

A manyan birane irin su Abuja mazauna unguwannin da suke maƙwabtaka da gidajen mai na ganin bone, kamar yadda muka samu bayanai daga mutane.

A misali babban titin Murtala Muhammad Way na hanyar Kubwa wanda ke ɗauke da manyan gidajen mai da dama, ya kan cushe da cunkoso saboda motocin da ke kan layuka.

Hakan yana jawo damuwa da matsalar ɓata lokaci ga ma waɗanda ba man za su saya ba.

Ga abin da wasu ke cewa:

2. Ƙarin kuɗin abin hawa da tsadar wasu abubuwan

Wata matsala ta biyu da al’umma ke kokawa a kanta ita ce ta yadda masu ababen hawa suka ƙara farashi.

A wasu wuraren ma ba farashin abin hawa ne kawai ya yi tashin gwauron zabi ba, har da na wasu abubuwan yau da kullum, kamar dai yadda wasu suka shaida mana.

Ga abin da wasu masu bin shafukanmu suka aiko mana:

3. Yini da kwana a layi
Babban tashin hankalin da ƙarancin rashin mai ya jawo wa ƴan Najeriya shi ne shafe lokaci da suke yi a gidajen man.

A wasu lokutan ma bayan mutum ya yini ya kwana, da zarar layi ya kusa zuwa kansa sai a ce man ya ƙare.

Wannan lamari na matuƙar tunzura mutane. Ga abin da wasu da dama ke cewa.

4. Tsadar man fetur – Ko da kuɗinka sai da rabonka

Lamarin man fetur ya zama ko da kuɗinka sai da rabonka. Tadarsa ta yi yawa ta kai intaha kamar yadda mutane da dama suke kokawa.

A wasu wuraren ma sai dai a sayi mai a hannun ƴan bumburutu, wadanda suke nunka kudin kowace lita sau uku ko huɗu kan yadda aka saba saya.

Ga bain da wasu suka shaida mana:

5. Dambe da zage-zage

Wannan shi ne abu mafi ɓata rai dangane da matsalar ƙarancin man.

Wasu gidajen man sun zma kamar filin dambe da kokawa duba da yadda faɗa ke rincabewa tsakanin masu saye da ke kan layi, sakamakon musun na riga ka, ko na ka sha gaba na.

Rabon faɗa ya zama shi ne babban abin da aka fi mayar da hankali a kai a wasu gidajen man. Har ta kai wasu gidajen kan rufe su dakatar da ba da man har sai komai ya lafa.

Matashiya
Najeriya ita ce ƙasar da ta fi kowacce arziƙin man fetur a Afirka, sai dai an shafe gwaman shekaru tana fama da samun matsalar ƙarancin man fetur akai-akai.

Hakan ya samo asali ne kan rashin matatun man fetur da ke cikin hayyancinsu a ƙasar.

Wannan ne dalilin da ya sa a dole ƙasar ke sayo tataccen man fetur daga ƙasashen wajen da take sayar musu da ɗanyen.

Batun shirin gwamnati na janye bayar da tallafin mai yana yawan jawo tarnaƙi a wajen samar da man.

Amma kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce wannan rashin man da ake fama da shi a yanzu ya samu ne saboda killace miliyoyin litocin gurbataccen man da ya yadu a kasuwa.

A yanzu NNPC ya ce yana shirin samar da lita biliyan 2.3 na fetur a fadin ƙasar – kuma cibiyoyin NNPC ɗin za su fara rarraba man ba dare ba rana a fa din ƙasar don samar da sauƙi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here