EndSars: Gwamnatin Najeriya ta ce ba a Kashe Kowa ba a Zanga-Zangar ta Bara

 

Gwamnatin Najeriya ta ce babu wata tartibiyar shaida da ke nuna cewa an kashe masu zanga-zanga a dandalin Lekki ranar 20 ga watan Oktoban 2020.

Ministan bayanai da al’adu Lai Muhammed ya shaida wa manema labarai a Abuja cewar binciken da masana kan harkokin makamai da rahotannin da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Amurka sun jaddada iƙirarin sojoji na cewa ba a harbi mai zanga-zanga ko ɗaya ba.

Ya ce gwamnatin Najeriya za ta yi aiki tare da hukumomin jahohi wajen biyan kuɗin fansa ga mutanen da yan sanda suka ci zarafinsu a ƙasar.

Ya kuma ce Majalisar Zartarwar ƙasa ta umarci jahohi su miƙa rahotonnin kwamitocin bahasinsu ga Antoni janar na jahohinsu don gaggauta gurfanarwa da yanke wa masu laifi hukunci.

A yau Laraba ne kuma ake gudanar da wata zangar-zangar don tunawa da ‘harbe-harben’ na Lekki da ake zargin sojoji sun yi a rana irin ta yau bara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here