Mutane 46 sun Rasa Rayukansu sanadiyyar Ambaliyar Ruwa a Indiya

 

Kimanin mutane arba’in da shida ne aka tabbatar da mutuwarsu, sakamakon ambaliyar da aka shafe kwanaki biyu ana yi a jahar Uttarakhand da ke arewacin Indiya.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya haifar da ambaliyar.

Masu aiko da rahotanni sun ce gidaje da dama sun nutse, hanyoyi da gadoji sun rufta.

Wani babban jami’in ‘yan sanda Nilesh Bharne, ya shaida wa BBC cewa ana ci gaba da aikin ceto a yankunan da abin ya shafa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here